Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Jam'iyyar PDP Ta Nemi DSS Ta Binciki Pantami

Daga Muhammad Farouk -Ta Nemi Shugaba Buhari Ya Kore Shi A Matsayin Minista  Jam’iyyar adawa ta PDP ta nemi hukumar tsaron farin kaya ta...


Daga Muhammad Farouk

-Ta Nemi Shugaba Buhari Ya Kore Shi A Matsayin Minista 

Jam’iyyar adawa ta PDP ta nemi hukumar tsaron farin kaya ta DSS da su yi hanzarin gayyatar ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami domin ya amsa tambayoyi kan zargin alakarsa da Taliban da kuma Al-Qaeda. 

Jam’iyyar har wala yau ta nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya cire ministan a mukaminsa duba da muhimmancin zargin da ake yi wa ministan. 

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a sanarwar da Kakakinta, Kola Ologbondiyan ya fitar a ranar Lahadi.

 “matakin jam’iyyarmu ya zo ne bisa damuwar da al’umma ta nuna a gaban duniya bisa zargin da ake yi wa ministan sadarwar, wanda yake da iko da muhimman bayanai, da ya hada da na daidaikun mutane da kuma na fitattu a cikin gwamnati da wajen gwamnati da kuma bangaren gargajiya da masu addini”, inji PDP. 

 “jam’iyyar PDP ta damu da wannan zargin da ake yi wa ministan a bayyane haka, inda ake zarginsa da cewa akwai yiwuwar ya bada kai bori ya hau dangane da rijistar lambar shaidar zama dan kasa (NIN) da ka iya bai wa masu kutse da da bata gari daga wadansu kasashen damar su yi rijista a matsayin ‘yan kasa”, suka lurantar.  

PDP ta karkare da cewa; “jam’iyyarmu na neman DSS da su yi bincike kan wannan zargin wanda ya haifar da rashin natsuwa musamman ma duba da yadda ayyukan ‘yan bindiga da sauran ‘yan ta’adda ke kara habbaka a kasarnan. Jam’iyyar PDP na shawartar ‘yan Nijeriya da su kasance ido bude a duk inda suke, tare da bada bayanan da ya kamata ga hukumomin tsaro domin bukatar kasarnan”, suka jaddada. 


No comments