Jaridar MADOGARA Ta Nemi Masu Wadata Su Taimakawa Mabukata A Lokacin Ramadana


Daga Wakilinmu

Kamfanin 5 Stars Media Services, masu lura da shafukan Jaridar MADOGARA, Madogara TV/Radio, Taskar Wasanni ta nemi masu wadatar arziki da na zuci da su taimakawa mabukata a wannan lokaci na Ramadana domin samun ladar dake cikin ciyar da mabukaci a watan.

Jaridar ta MADOGARA ta nemi hakan ne a cikin sakon taya murnar shiga watan Ramadana da ta saki da yammacin ranar Litinin 12 ga watan Afrilun 2021, wanda Babban Editan Shafin www.madogara.com.ng ya sanyawa hannu, inda ya ce lokacin Ramadana lokaci ne har wala yau na neman tuba ya zuwa ga Allah ta'ala.

Takardar mai taken; 'ALLAH YA KARBI IBADUNMU' ta fara ne da cewa; "Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar Na III a cikin daren yau Litinin ya sanar da cewa a gobe Talata ne 1 ga watan Ramadan 1442, hakan ya biyo bayan tabbacin ganin jinjirin wata da aka samu a sassa daban-daban na kasarnan", ya bayyana.

Ya ci gaba da cewa; "a madadin kafatanin ma'aikatan Jaridar Madogara, Madogara TV/Radio , Taskar Wasanni  na taya dukkanin al'ummar Musulmi murnar shiga watan Ramadana", inji shi.

Ya kara da cewa; "muna kuma addu'ar Allah ta'ala ya karbi ibadunmu baki daya, ya sa a gafarta mana dukkanin zunubanmu a cikin wannan wata na Ramadana", ya tabbatar.

Sannan sun nemi al'umma su ribaci watan da neman gafara, inda suka ce; "Muna kuma amfani da wannan dama wajen tunatar da al'umma cewa, su yi amfani da wannan lokaci na Ramadana wajen neman gafarar Allah da kuma yiwa kasarmu addu'ar samun zaman lafiya da yalwar arziki". 

Sun yi kira da babban murya ga dukkanin masu wadatar arziki da na zuci, da su yi amfani da wannan wata wajen ciyar da mabukata. Domin ya zo a ruwaya cewa ciyarwa a wannan wata ko da da kwayar dabino ne, akwai dimbin lada a cikinsa.

"Muna kuma amfani da wannan dama wajen kira ga 'yan kasuwa da su sassautawa al'umma a cikin wannan wata domin samun Rahamar Allah, ka da kuma su tsawwalawa kayayyakin masarufi kudade", ya lurantar.

A karshe sun karkare da cewa; "muna kira ga dukkanin shugabanni a matakin kasa, jiha, kananan hukumomi da gunduma, da su tallafawa al'ummar kasa baki daya, tare da gudanar da mulki bisa adalci ga kowa ba tare da nuna bambancin addini, siyasa, kabila ko jinsi ba. Allah ta'ala ya karbi ibadunmu baki daya". 

Post a Comment

0 Comments