Jihar Kaduna ta tara sama da naira biliyan 50 a 2020 inda ta kasance ta biyar a jerin jihohin da suka fi samun kuɗaden shiga, kama...
Jihar Kaduna ta tara sama da naira biliyan 50 a
2020 inda ta kasance ta biyar a jerin jihohin da suka fi samun kuɗaden shiga,
kamar yadda rahoton hukumar ƙididdiga ta Nijeriya NBS ya bayyana.
Rahoton
ya ce jihar Kano cibiyar kasuwancin arewacin Nijeriya ta kasance matsayi na
takwas a jerin jihohin inda ta tara sama da naira biliyan 31.
Hakan na
nufin jihar Kaduna ta ba jihar Kano tazarar kusan naira biliyan 19.
Rahoton
ya ce jimilar naira tiriliyan 1.31 jihohin na Najeriya suka tara a 2020, amma
adadin ya yi ƙasa idan aka kwatanta da 2019 inda suka tara naira tiriliyan
1.33.
Jihar
Legas ce ta farko inda ta samu sama da naira biliyan 418, jihar Rivers ce ta
biyu da ta samu sama da naira biliyan 117, sai birnin tarayya Abuja a matsayin
na uku da ya samu sama da naira biliyan 92.
Jihar
Delta ce ta huɗu inda ta samu sama da naira biliyan 59 a 2020.
Ogun da
ke matsayi na shida ita ke bi wa Kaduna inda ta tara sama da naira biliyan 50.
Jihar
Yobe ce ta ƙarshe a jerin matsayin jihohin na tara kuɗaɗen shiga a jihohinsu.
No comments