Jihar Katsina Za Ta Sanya Zaratan Karnuka Su Yi Gadin Makaranta Kwana


Gwamnatin jihar Katsina ta shirya tsaf domin siyan zaratan karnuka da za ta raba su zuwa makarantun kwana na Sakandaren dake fadin jihar baki daya.

Kwamishinan ilimin jihar Katsina, Farfesa Badamasi Lawal Charanchi shi ne ya tabbatar da hakan, kamar yadda MADOGARA ta labarto.  

Kwamishinan ya bayyana kowace makarantar kwana za ta sami manyan karnuka masu kaifin basira a kan duk wani motsi, wanda haushinsu zai taimaka wajen ankarar da daliban kwanan da masu tsaronsu cewa akwai abin da ke shirin faruwa. 

Post a Comment

0 Comments