Jinjina Ga Gwamna Bala Muhammad: Garkuwan Fulanin Nijeriya


 Daga Musa Gambo Yakana

Sanin kowa ne an dauko hanyar bata kima da dajarar Fulani a sassan kasar nan, wanda har ta kai wasu na kallon Fulani kawai a matsayin ‘yan tayar da hankali ko masu neman fitina ko wasu ‘yan ta’adda.

A irin wannan lokacin da irin wannan gabar ne, Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi ya ce a’a a tsaya a yi dubiya a nemo ina matsalar take ina kuma mafita, ba kawai a dauki Fulani Makiyaya ana danganta su da laifukan da kila ma ba laifinsu ba ne, ya kuma sake lura da yadda wasu gwamnoni ke fakewa da batun garkuwa da mutane wajen neman cin mutuncin Fulani da makamancin hakan.

A bisa fitowa bainar jama’a da warware zare da abawa da Gwamna Bala Muhammad ya yi a kwanakin baya, an samu natija sosai kuma hakan ya rage wa Fulani zaman dardar da suke yi a yankunan kasar nan musamman Kudu.

Kodayake wasu bata gari sun so juya wa Gwamna Bala Muhammad asalin abun da yake nufi da inda ya dosa, inda wasu suka nemi cewa yana marawa wa daukan makamin Fulani; alhali ba hakan yake nufi ba.

Gwamna Bala ya fito ya kare Fulani ne a fannonin da tabbas idan duk mai hankali ya zauna ya yi nazari zai gane ina aka dosa.

A kowace kabila ana iya samun baragurbi, amma a ce kabila gaba dayanta ake neman a shafa mata bakin fenti wannan ba daidai ba ne tattare ma da cewa asalin abun da ake harsashe ko tunanin ba haka yake ba.

Idan mutum ya dauko tarihin Fulani zai gaskata ni cewa mutane ne masu son zaman lafiya da kwanciyar hankali. A da can baya in ka ji rikicin Fulani za ka tarar tsakanin manomi ne da makiyayi wanda kuma a lokuta da dama akwai matakan da ake bi wajen shawo kan irin wannan rashin jituwar nasu.

Amma a yau an wayi gari wasu dauke da bindiga sai a danganta da Fulani, kama-kama har ana neman maida Fulani wasu ‘yan ta’adda; kuma a zahirin gaskiya ba a yi wa kabilar Fulani ma adalci, idan an samu mutum dan kabilar Fulani ya yi laifi, a maimakon a ce ‘Wane’ sai a ce Fulani ne, wa kabilar Fulani kadai ake wannan cin mutumcin. Idan dan Igbo ko wata kabila ya aikata laifi sai ka ji an kira sunansa kai tsaye. Irin wadannan misalan duk suna kara fito mana da boyayyar manufar neman bata wa Bafulatani suna.

Kuma a dauki wannan a ajiye ma a gefe, Gwamna Bala Muhammad a wani taron da kungiyar wakilan kafafen yada labarai ta shirya a Bauchi kwanaki, ya fito ya nuna irin yadda ake mugunawa da cin mutumcin Fulani wanda har ya nemi a daina hakan, wannan ya fito wa duniya da cewa gwamna Bala garkuwa ne ga Fulani.

Gwamnan ya yi furuci ya ce; “Ya kamata al’umma ta tausaya, ya kuma kamata al’umma ta yi alhini da dogon tunani kan yadda ake rikon sakainan kashi  da mutunci da kuma yadda ake mu’amala da ‘yan uwa Fulani a cikin daji.”

Ya kuma ce ya kamata al’umma ta yi la’akari da irin cin mutuncin da ake yi gami da cin zarafinsu da ake yi, kashesu da ake yi irin kisa na gilla, da yadda ake kai musu farmaki a kwashe musu shanu da yadda ake kai musu hare-hare a karkashesu, wasu lokutan ma a kashesu shanunsu su bata dangi su bata a nemesu a rasa. Barnar da dai ga su nan daban-daban kuma bila’adadin.

A bisa wannan ne gwamnan ya ce lokaci ya yi da ya kamata a dubi wadannan bayin Allah da suke cikin daji, ba su da wutar lantarki, ba su da kwalta, ba su da asibitoci, ba su da wani wajen da za su je su kai kukansu; a cikin daji suke amma ba a barsu sun sarara ba.

Inda suka zauna zama suke yi na dan sati biyu, uku su matsa zuwa can wurin da akwai dan yabanya su kai dabbobinsu, su sake tashi daga nan su matsa zuwa can, amma duk da hakan dan abun da bai taka-kara ya karya ba, ana cin zarafinsu. Ya ce ya kamata al’ummar Nijeriya, musamman ma gwamnati ya kamata su dubi wannan lamarin da idon basira saboda, dalilin da ya sanya kalilan daga cikinsu in ka ga suna tafiya za ka gansu rike da bindiga, ba wai son kansu ba ne, sun yi ne domin gwamnati ta kasa bada kariya, ta kasa baiwa wadannan mutanen dauki, a kashesu yau, a bindigisu gobe, a kwashe musu shanu jibi, har ya kasance babu wani abun da ake yi musu na kawo dauki wanda ya kasance hakkin gwamnati ne ta samar wa kowani dan kasa tsaro  gwargwadon hali.

Da aka samu akasin tsaro, aka samu matsala na rashin tsaro, kuma wadannan mutanen ana kashesu sosai, hakan ya sanya shi ya ce ba laifinsu ba ne, nan da can in an gansu suna kare kansu.

Amma sam bai fito ya ce yana talla wa sauran ‘yan Nijeriya ko sauran Fulani lallai sai kowa ya dauki makami AK-47 yana tare da shanunsa don ya yi kiwo ba.

Irin wannan namijin kokarin da Gwamna Bala Muhammad ya yi ya sanya an fara samun natija wajen daina danganta Fulani da laifukan ta’addanci.

Wannan ya zama kalubale ga sauran shugabanin Arewa, musamman gwamnoni, da rawar da za su iya takawa wajen daidai lamura da neman wanke Fulani daga irin wannan bakin fentin kafin lokaci ya kure musu.

Tabbas Gwamna Bala Muhammad ya kasance irin shugabannin da talaka ke nema ruwa a jallo da fatan samu. Daga lokacin da ya zama gwamnan jihar Bauchi zuwa yanzu, ya isa samar da dumbin ayyukan raya jihar Bauchi da kyautata.

Idan muka duba fannin shimfida ayyukan raya jihar, ya iya samar da manyan titina da wadanda aka kammala da wadanda ake kan aikinsu a halin yanzu, ayyuka ne kuma ake yi irin na Mahdi ka ture masu nagarta ga kuma gadoji da kwalbati-kwalbati na gani a fada.

A bangaren walwala a jihar sai sambarka, sannan gwamnan yayi kokarin dawo da kaunan gwamnati a zukatan talaka domin babu wata shiyya ko yanki a Bauchi da yanzu ba ta shaidar aikin gwamnati mai ci.

A fannin ilimi, ruwan sha, noma da kiwo dukkaninsu gwamna Bala Muhammad na kokari wajen ganin ya fitar da jihar Bauchi kunya. uwa-uba ga irin kokarin da yake yi wajen jawo kamfanonin zuba jari domin su zuba jarinsu a jihar Bauchi, tabbas wannan sa’ayin zai baiwa dumbin matasa damar samun guraben ayyukan yi. Bala ya cancanci yabo matuka.

Musa ya rubuto mana ne daga Unguwar Kaura, cikin birnin Zariya

Post a Comment

0 Comments