Jirgin Sojin Saman Nijeriya Ya Yi 'Kuskuren' Luguden Wuta Kan Sojin Kasa


Daga Muhammad Farouk

Rahotanni daga jihar Borno na nuni da cewa; akasarin sojin da suka mutu sakamakon harin Boki Haram a Mainok da ke Jihar Borno sun mutu ne sakamakon harin sama da jirgin yakin Nijeriya ya kai musu cikin kuskure.

Bayanan da ke zuwa na nuna cewa yayin da wasu daga cikin sojojin suka rasu sakamakon artabu da mayakan Boko Haram akasarin su sun mutu ne sakamakon harin da jirgin sojin ya kai musu, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta bayyana cewar ana yada faifan bidiyon yanzu haka a kafofin sada zumunta.

Kakakin rundunar sojin saman Nijeriya, Edward Gabwet ya shaidawa Jaridar cewar shi ma ya ga bidiyon amma ba zai iya tabbatar da afkuwar lamarin ba.

Jami’in ya ce za su gudanar da bincike idan sun tabbatar da sahihancin bidiyon za su kaddamar da bincike kan lamarin.

Wannan shi ne kazamin hari na baya-bayan nan da ya ritsa da sojojin Nijeriya wadanda ke yaki da boko haram a arewa maso gabashin kasar.

Post a Comment

0 Comments