Ka Da Ku Alakanta Pantami Da Mutuwar Yakowa -CAN Ta Yi Gargadi


Kungiyar Kiristocin Nijeriya reshen Jihar Kaduna ta bukaci 'yan kasar da su nesanta ministan sadarwa Dr Isa Ali Pantami daga hadarin da ya yi sanadiyyar mutuwar tsohon Gwamnan Jihar Ibrahim Yakowa.

Yayin da yake mayar da martani kan zargin da ake yiwa ministan cewar ya jagoranci wani taron dake adawa da zaman Yakowa Gwamnan Kaduna, shugaban kungiyar John Hayab ya bukaci 'Yan Nijeriya su yi watsi da wannan zargin.

Hayab wanda shi ne mai baiwa Yakowa shawara kan harkokin addini lokacin mulkinsa ya ce a matsayinsa na wanda yake kusa da Marigayin bai dace a danganta rasuwar tsohon gwamnan da ministan ba, inda yake cewa yin haka zai jefa zaman lafiyar Nijeriya cikin hadari.

Dole a kawo karshen wasu kasidu dake naman kawo tashin hankali

Shugaban kungiyar ya bukaci jami’an tsaro da su tashi tsaye wajen kawo karshen kasidun da yanzu haka a rabawa a cikin kasar wadanda ke neman tunzira tashin hankali, yayin da ya ce kungiyar da iyalan Yakowa ba su ji dadin abin da ke faruwa ba.

Hayab ya ce duk wadanda ke tunanin cewar suna da wasu bayanai da za su taimakawa jami’an tsaro gudanar da bincike kan aikata wani laifi suna da hurumin yin haka bisa yadda doka ta tanada.

Shugaban kungiyar ya ce a matsayinsa na shugaba ya yi magana ne saboda hakan ya zama wajibi, amma bai dace a ce saboda baka son mutuum ba sai ka goyi bayan zargin da aka masa wanda bashi da makama balle tushe.

Post a Comment

0 Comments