Ka Sanya Dokar-Ta-Baci A Bangaren Tsaro –Rokon Majalisa Ga Buhari

 


Sakamakon ci gaba da tabarbarewar tsaro a Nijeriya, Majalisar Wakilan kasar ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa dokar-ta-baci a bangaren tsaro da zummar dakile matsalar tare da tabbatar da zaman lafiya a fadin kasar baki daya kamar yadda gidan Rediyon Faransa ya labarto.

Yayin zamanta na jiya majalisar wadda ta jaddada matsayinta na ci gaba da dorewar Najeriya a matsayin kasa guda ta bayyana shirin gudanar da wani taro na musamman dangane da yanayin tsaron kasar wanda zai kunshi duk masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro.

Majalisar ta kuma gayyaci mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da hafsoshin tsaron kasa da shugabannin hukumomin tsaro daban-daban da shugaban Hukumar Kwastam da Daraktan Hukumar Kula da Leken Asiri ta kasa domin yi mata bayani kan halin da kasar ke ciki.

Majalisar ta kuma bukaci bangaren shari’a da ya gaggauta matakan da yake dauka wajen yi wa wadanda ake zargi shari’a kan laifin da suka shafi hare-haren 'yan bindiga da ayyukan ta’addanci domin ya zama darasi da jama’a.

A karshe majalisar ta bukaci gaggauta kai dauki wajen tallafa wa daukacin jama’ar da suka fuskanci ire-iren wadannan hare-hare a fadin Nijeriya.


Post a Comment

0 Comments