Daga Muhammad Farouk Ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed ya zargi 'yan Nijeriya da kafafen watsa labarai a matsayin...
Daga Muhammad Farouk
Ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed ya zargi 'yan Nijeriya da kafafen watsa labarai a matsayin wadanda suka sanya kamfanin Twitter ya ki kawo Hedikwatarsa ta Afrika zuwa Nijeriya ya kai kasar Ghana.
A ranar Litinin ne kamfanin Twitter Inc ya ayyana cewa zai bude ofishinsa a kasar Ghana, lamarin da ya sanya 'yan Nijeriya da dama a bangaren kimiyyah da fasaha suka bayyana shi a matsayin gagarumar asara da Nijeriya ta yi.
Da suke bayyana rashin jindadinsu a shafukan sada zumunta, wadansu ba'adin Nijeriya sun yi zargin cewa matakin Twitter na kai ofishinta Ghana yana da alaka da tsarin gudanar da kasuwanci a karkashin gwamnatin Buhari kamar yadda MADOGARA ta nakalto.
Sai dai da yake maida martani a ranar Alhamis, Lai Mohammed ya wanke gwamnatin tarayya daga wadannan zarge-zarge, inda ya ce yana fatan 'yan Nijeriya za su so kasar su, sannan su zama masu kishin kasa domin daukaka martabar kasar su.
Lai Mohammed ya ce yadda 'yan Nijeriya suka bakanta kasar a idon duniya a shafukan sada zumunta a lokacin zanga-zangar EndSARS na daga dalilan da ya sanya Twitter ba ta kawo ofishinta Nijeriya ba.
"Dalilan Twitter na zabar yin Hedikwatar ta a birnin Accra ta kasar Ghana, shi ne Accra sune jigon Dimokuradiyya kuma akwai doka da oda a kasar da sauran dalilai", inji shi.
Ya ci gaba da cewa; "wannan shi ne abin da zaka samu idan ka bakanta kasarka a idon duniya", ya tabbatar.
"Kafafen watsa labarai sune ababen zargi wanda a kowanne lokaci suke kambama kulen da kasar ke fuskanta", ya labarta.
"Musamman ma lokacin zanga-zangar EndSARS, inda a lokacin 'yan jaridar Nijeriya na jaridu da talabijin da Rediyo da kuma sabbin kafafen watsa labarai suka yi aiki tukuru wajen nuna Nijeriya a matsayin wata wutar jahannama da ba wanda ke son rayuwa cikinta", inji shi.
"suka hada hannu baki dayan su domin su bakanta ba kawai gwamnati ba har ma 'yan Nijeriyar baki daya", a cewar Lai Mohammed.
Ministan ya ce yadda ake ci gaba da tattauna matsalolin kasarnan hakan ne ya sanya Nijeriya ke rasa wadanda za su zo su zuba hannun jarinsu a kasar, wanda hakan ke sanya da dama su rasa ayyukan yi.
"Ba wai muna cewa ka da ku caccaki gwamnati bane, amma a yi shi cikin gaskiya da kishin kasa. Idan ka tarwatsa gidanka, ina zaka je ka rayu?", Ya tambaya.
"Ku yi tunanin ayyukan da 'yan Nijeriya za su samu da a ce Hedikwatar Twitter Inc a Nijeriya za a yi ta, da kuma irin gudummawar da hakan da zai bai wa Nijeriya, amma mun tarwatsa wannan damar", ya bayyana cikin takaici.
No comments