Karairayi MURIC Kawai Ta Shirya Kan Majalisa Ta Takwas, Inji Saraki


Jaridar Leadership A Yau  ta labarto cewa; tsohon Shugaban Majalisa ta Takwas a Majalisar Dattawan Nijeriya, Dr. Abubakar Bukola Saraki ya mayar da martani kan wani ikirari da Shugaban kungiyar MURIC, Farfesa Ishak Akintola ya yi.

Tsohon Shugaban Majalisar ta Dattawa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kwara, Dr. Saraki ya bayyana wannan sanarwar manema labarai da MURIC din ta fitar a matsayin ‘farfaganda mai cike da yarfe da karairayi. Saraki ya fadi haka ne yau a Abuja a wata takardar manema labarai mai dauke da sa hannun Oluwole Onemola, daya cikin masu taimaka masa kan harkar yada labarai.

Saraki ya ce, batun da Farfesa Ishak Akintola ya fitar na cewa Majalisa ta Takwas ce ta dakile yunkurin Shugaba Buhari na son sayo makaman Dala Biliyan 1, ba komi ba ne face kokarin maye gurbin gaskiya da karya. “Wannan zunzurutun karya ne. Ba a taba yin wani lokaci da Majalisa ta takwas ta dakile yunkurin fitar da kudi don sayo makamai ba, mun dai dage akan cewa duk wani kudi da za a fitar dole ne a bi ka’idar da ta dace.”

Dr. Saraki ya jaddada cewa: “A ranar Laraba 25 ga watan Afrilun 2018, a matsayina na Shugaban Majalisar Dattawa na karanta wasika a gaban Majalisa daga Shugaban kasa Muhammadu Buhari wacce a cikinta ya nemi a sakar masa kudi cikin gaggawa wanda sun kai dala 496,374,470. An ce kudin za a biya su ne kai tsaye ga asusun gwamnatin Amurka.

“Sai dai kuma a kundin tsarin mulkin Nijeriya wanda shi ne madogarar duk wani aiki da muke yi, a cikin wannan kundin an zayyana cewa duk wani abu da ya shafi irin wannan harkar yana karkashin kulawar majalisar kasa ne. Kuma babu inda aka ce shugaban kasa zai ba majalisa irin wannan umurnin. Wannan na nuni da cewa, tun farko Shugaban kasa bai bi ka’idar da ta dace ba. Amma duk da haka Majalisa ta bayar da umurnin sakin kudin. Kudin da MURIC ke magana wato Dala biliyan 1, Majalisa ta takwas ta bada umurnin sakinsu.

“Haka nan kuma idan ana iya tunawa, Gwamnatin Amurka ta yanke hukuncin daina sayar da manyan makamai ga Nijeriya bisa zargin take hakkin dan Adam daga bangaren sojojin Nijeriya. Bisa wannan ne ma wakilan majalisar Amurk suka zo Nijeriya a ranar 28 ga watan Agusta inda suka zauna da wakilan Majalisar Nijeriya; a nan ne muka roke su da a janye wannan hukuncin kuma za mu yi bincike kan zargin tare da tabbatar da rashin afkuwar irin haka a gaba.

“Sai bayan wannan zaman da muka yi da wakilan Majalisar Amurka bisa jagorancin Sanata Chris Coons da Ambasada Symington sannan Amurka ta yarda ta janye dokar daina sayar da makamai ga Nijeriya. Kuma bayan zaman namu ne, Majalisar Amurka ta ba Shugaba Trump shawarar a sayarwa da Nijeriya jiragen yaki na TUCANO.” Inji shi.

Ya kara da cewa, daya daga cikin kokarin Majalisa ta 8 ne ya sa a lokuta da dama suka gayyaci shugabannin bangarorin tsaro su bayyana gaban Majalisa don a tattauna irin gudummawar da suke bukata a fagen daga.

“Misali a ranar 3 ga watan Fabrairun 2016 shugabancin majalisa ta takwas ya zauna da shugabannin bangarorin tsaro. Haka ma a ranar 8 da 12 ga watan Fabrairu Majalisa ta 8 ta shirya wani taro na musamman kan tsaro wanda cikin mahalarta taron akwai Mai ba shugaban Kasa Shawara kan harkar tsaro, Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da sauran shugabannin bangarorin tsaro.

Daga karshe dai tsohon Shugaban Majalisar ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi watsi da zantukan MURIC, domin cike suke da son rai, yarfe, da ajandar bata suna.


Post a Comment

0 Comments