Tsohon Gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu ya bayyana dalilin da ya sa Gwamnonin Jam’iyyar PDP suka bijirewa tsohon shugaban kasa Goo...
Tsohon Gwamnan Jihar Neja, Babangida
Aliyu ya bayyana dalilin da ya sa Gwamnonin Jam’iyyar PDP suka bijirewa tsohon
shugaban kasa Goodluck Jonathan a shekarar 2015 lokacin da ya tsaya takarar
neman wa’adi na biyu.
A wata sanarwar da ya rabawa manema
labarai, tsohon Gwamnan ya ce sun dauki matakin ne saboda karyar alkawarin da
ya yi cewar ba zai tsaya takara ba bayan kamala wa’adin tsohon mai gidansa
Umaru Yar’adua da kuma samun nasarar zaben shekarar 2011.
Babangida ya ce daukacin gwamnonin
sun marawa Jonathan baya lokacin da ‘Yar Adua ya rasu da kuma takararsa ta shekarar
2011, amma hakikancewarsa cewar zai zarce a shekarar 2015 ya gamu da fushin su
domin hakan ya saba ka’ida kuma hakkinsa ne a matsayin shugaban gwamnonin
arewacin kasar ya fito ya yi bayani akai kamar yadda rahoton RFI Hausa ya
labarto.
Tsohon Gwamnan ya ce ba wai sun
nunawa Jonathan kiyayya bane, sai dai sun dauki matakin ne domin kare muradun
jama’ar yankin dangane da alkawarin da suka yi a rubuce wanda aka sanya hannu
akai cewar tsohon shugaban ba zai sake takara ba.
Babangida Aliyu ya ce abin takaici
ne da yau za a kira sunansa ana cewa shi ne yake adawa da takarar Goodluck
Jonathan a shekarar 2015.
Yanzu haka dai Jam’iyyar PDP a
karamar hukumar Chanchaga ta dakatar da tsohon Gwamnan saboda abin da ta kira
zagon kasa da kuma wasu harkoki da suka sabawa Jam’iyar ta su.
No comments