Kiristoci Sun Yi Zanga-zangar Goyon Bayan Pantami

 


Kungiyar Malaman kiristoci ta ‘Christian Bishops and Clergy Council’ ta nuna goyon bayanta ga shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa goyon bayansa ga ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ali Pantami bisa zargin ministan da goyon bayan ta’addanci a shekarun baya.

Kungiyar ta bayyana goyon bayanta ne a gangamin da ta shirya a dandalin neman ‘yanci na Unity Fountain dake birnin tarayya Abuja. Inda suka bayyana cewa wadanda suke daukar nauyin zargin ministan wadansu kusoshi ne da canje-canjen da ministan ya kawo ya shafe su.

Malaman kiristocin sun kasance suna dauke da takardu da kwalaye da suka daga wanda suke rubuce-rubucen goyon bayansu ga shugaba Buhari tare da bayyana shi a matsayin shugaban da ya hada kan kasa.

Kungiyar ta jaddada cewa shugabannin kiristoci sun gudanar da gangamin ne domin nuna goyon bayan su da tattauna zaman lafiya domin samun hadin kan kasa da kuma nuna goyon baya ga shuganni a kasar.

Da yake jawabi a wurin gangamin, shugaban kungiyar Bishop Abel King ya ce fitowarsu ya zama dole ne sakamakon yadda suka ga kowa na bayyana ra’ayinsa kan zargin ministan.

 


Post a Comment

0 Comments