Ko PSG Za Ta Bar Neymar Ya Koma Gida Ya Buga Wasannin Olympic?


Hukumar kwallon kafar Brazil ta mikawa PSG bukatar baiwa dan wasan gabanta Neymar Jr damar taka leda a wasannin da kasar za ta fafata yayin gasar Olympic a Tokyo.

A wata zantawar kocin na Brazil da jaridar wasanni ta Globo, ya ce Neymar na daga cikin ‘yan wasansu sahun gaba da su ke fatan su taka leda yayin gasar ta Olympic ganin irin bajintar da ya nuna a makamanciyar gasar cikin shekarar 2016 a Rio de Jannero.

Sai dai shi da kansa da Kocin na Brazil ya ce abu ne mai wuya PSG ta amince da bai wa dan wasan dama la’akari da yadda ya ke shirin taka leda a gasar Copa America tsakanin ranekun 13 ga watan Yuni zuwa 11 ga watan Yuli.

Gasar ta Olympic dai za ta fara ne kwanaki 10 bayan Copa America kuma za a kammala ta ranar 8 ga watan Agusta wato kwanaki 2 bayan bude sabuwar kakar gasar Ligue 1 a Faransa wanda ke nuna abu ne mai wuya PSG ta baiwa dan wasan dogon hutu na tsawon kwanakin.

Karkashin dokokin kungiyoyin Turai dai kowanne Club na da damar hana dan wasan halartar kowacce irin gasa matukar ba FIFA ce ta shirya ba.

Post a Comment

0 Comments