Ku Ajiye Batun Ballewa, Ku Taimaka Min Na Gyara Nijeriya –Sakon Tinubu Ga Inyamurai Da Yarbawa

 


Jigo a jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Ahmed Tinubu ya yi kira ga Inyamurai da Yarabawa da su hade da shi wajen ‘yantar da Nijeriya daga halin da ta fada na rashawa.

Tinubu ya yi wannan kiran ne a yayin da yake ganawa da manema labarai a garin Legas, inda ya nemi jagororin da suke jagorancin ballewar kasar Biyafara a bangaren Inyamurai da kuma kasar Oduduwa daga bangaren Yarabawa da su janye wannan fafutikar.

Asiwaju Tinubu, wanda ake yi wa kirari da Jagaban a karshen shekarar da ta gabata ya yi kira makamanciyar wannan, inda ya ce Inyamurai da suke rayuwa a Legas da su manta da batun kasar Biyafara su hada hannu da APC wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Har wala yau Tinubu ya ce lokacin sake rubuta tarihin Nijeriya yanzu ne, shiyasa ma yake kira ga ‘yan Kudancin kasarnan da su manta da batun ballewa su hada hannu da shi wajen ciyar da kasarnan zuwa gaba.

A cewarsa; “ina kira ga masu fafutikar kafa IPOB da Oduduwa da su kwantar da hankalinsu, su ajiye makamansu da fushi domin ciyar da Nijeriya gaba”, inji shi.

Ya ci gaba da cewa; “kasarnan duka ta mu ce. Kuma aikinmu ne mu tabbatar da komai na tafiya daidai. Babu wanda zai yi mana. Shiyasa akwai bukatar mu hada hannu da karfe wajen ganin abubuwa sun tabbata daidai. IPOB da Oduduwa su ajiye wannan fafutikar domin kudanci su samu damar fitar da shugaba a zaben 2023”, ya lurantar.

 

Post a Comment

0 Comments