Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Ku Rika Tunawa Da Masu Lura Da Makabarta Idan Za Ku Yi Alheri -Sakon Sanata Shehu Sani Ga 'Yan Siyasa

Daga Muhammad Farouk MADOGARA ta labarto cewa; tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bai wa 'yan siyasa sh...Daga Muhammad Farouk

MADOGARA ta labarto cewa; tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bai wa 'yan siyasa shawara akan su rika tunawa da masu aikin makabarta a yayin da za su yi wani aikin alheri, kyauta ko alfarma. Ba wai sai an muku mutuwa ku rika tunawa da su ba. 

Sanata Shehu Sani ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook, inda ya wallafawa cewa; "mafi yawancin lokuta kuna mantawa da masu aikin makabarta a lokacin da kuke yin alheri, kyauta ko alfarma. Sai kun mutu ko an maku mutuwa kuke tunawa da su", inji shi.

Sanatan ya ci gaba da cewa; "gashi kuma su suke kula da kabarin iyayenku. Da an maku mutuwa sai ku zo makabarta da manyan motoci, da kun tafi ba za su kara ganin ku ba. Idan kuka bari suka yi yajin aiki za ku koyi haka rami da diga", ya nusasshe. 

Ya karkare da cewa; "ku 'yan siyasa ku dai dunga tunawa da Excon makabarta. A dai duba". 

No comments