Sakataren
harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya gargaÉ—i kasashen Afrika a kan rawar da Chana ke takawa
a nahiyar, yayin da ya lashi takobin ƙarfafa ƙawancen Amurka da Nijeriya da
kuma Kenya.
Sakataren
Amurkan ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da ya kawo wa Nijeriya ta Intanet
sakamakon kullen Korona da aka yi.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken
ya tattauna da shugabannin ƙasashen biyu kuma yana 'rangadi' a wasu wurare ciki
har da asibitin tafi-da-gidanka da Amurka ta gina.
A lokacin da
yake amsa tambayoyin wasu mata Æ´an Afrika waÉ—anda suka yi karatu a Amurka,
Mista Blinken ya ce yana fata ƙasashen Afrika za su ƙulla ƙawance cikin hikima.
"Ba mu ce
kowa ya zaɓa tsakanin Amurka da China ba, amma muna ƙarfafa maku gwiwa kan ku
riƙa yin tambayoyi masu tsauri, ku yi bincike da kyau sannan ku buƙaci
gaskiya," a cewarsa kamar yadda BBC ta labarto.
Dangantakar da
ke tsakanin Amurka da Chana na ƙara tsami, kuma wannan ya haifar da zuba jari a
Afrika ta hnayar mayar da hankali kan albarkatun ƙasa.
Haka kuma,
Blinken ya yi magana kan yadda ƙasashen Afrika da dama ke fama da nauyin bashin
China da suka karɓa.
Ya ce ya kamata
ƙasashen Afrika su riƙa tunani mai zurfi idan wasu ƙasashen suka shigo ƙasarsu
don gina manyan ayyuka tare da zuwa da ma'aikatansu.
"Me ya sa
ba sa bai wa mutanen ƙasar da za su zuba jarin ayyukan yi?" a cewarsa
A nasa ɓangaren,
Shugaba Muhammadu Buhari a lokacin da yake magana da Blinken ya yi wa Shugaba
Biden godiya bisa sassauta takunkumin da Trump ya sa wa Æ´n Najeriya kan
takardun shiga Amurkar.
Shugaba
Buhari ya sha alwashin ƙarfafa ƙawance tsakaninsa da Amurka musamman a yankunan
da ke fama fda matsalar tsaro ciki har da yankin Sahel.
0 Comments