Kungiyar ‘Concerned Nigerians’ Ta Kai Karar Pantami Wurin Amurka

 

Daga Muhammad farouk 

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta ‘Concerned Nigerians’ ta rubuta takardar korafi zuwa ga ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya kan ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani bisa zarginsa da bayyana wadansu kalamai dake goyon bayan ‘yan ta’adda.

Takardar korafin jagoran kungiyar, Deji Adeyanju ne ya sanya mata hannu, ina ya gabatar da ita ga ofishin Jakadancin Amurka din a Nijeriya.

Ministan Nijeriya da tattalin arzikin zamani, Sheikh Isa Ali Pantami an sanya sunansa a cikin takardar korafin da aka aikawa ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya, inda aka yi korafin cewa ministan yana goyon bayan ‘yan ta’adda.

A bayanin korafin cikin takardar, an nuna yadda Ministan ya goyi bayan wadansu kungiyoyin ta’addanci a jawabansa da ya rika a baya. Inda aka yi zargin cewa a daya daga cikin jawabansa, ministan ya bayyana yadda yake jin farin ciki idan aka kashe ‘kafirai’.

Takardar korafin ta yi zargin cewa; ministan ya bayyana goyon bayansa ga kungiyoyin ta’addanci na Al-Qaeda da Taliban.  

Takardar ta ce; Pantami ya jinjinawa Osama Bin Laden, inda yake bayyana shi a matsayin jarumi kuma gwarzo kuma musulmi nagari da ma ya fi Pantami din.

Takardar ta nemi kasar Amurka da ta binciki zarge-zargen da ake yi wa ministan tare da sanya shi cikin jerin ‘yan ta’adda da Amurka ke nema idan aka tabbatar da zarge-zargen da ake yi masa.

Ofishin Jakadancin na Amurka ya karbi takardar korafin, inda suka sanya hannu kamar yadda Deji Adeyanju ya tabbatar.
 


Post a Comment

0 Comments