Majalisar Dattawa Ta Nemi Gwamnoni Da Su Bai Wa Ma’aikatar Shari’a Cin Gashin Kanta

 


A ranar Litinin fafutukar da ma’aikatan sashen shari’a ke yi ta neman cin gashin kai ga sashen ta samu tagomashi daga Majalisar Dattawa, inda majalisar ta bukaci gwamnonin jihohin kasar nan su tabbatar wa da sashen na shari’a cin gashin kansa.


Shugaban kwamitin majalisar dattijai kan harkokin shari’a da ‘yancin Dan Adam, Sanata Opeyemi Bamidele, ya fada wa gwamnonin cewa tabbatar wa da sashen shari’a hakkinsa na cin gashin kai abu ne da ya zama wajibi amma ba shawara.


Bamidele ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai bayan wani taron jin ra’ayoyin jama’a da kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattijai kan harkokin shari’a da ‘yancin dan’Adam da na sojojin ruwa da na safarar jiragen ruwa kan bindigogi suka shirya.


An saurari koken ne a kan dokar 2004 da aka yi wa Kwaskwarima a 2021 da Dokar Yankin Tattalin Arziki na Musamman 2010 (Sokewa da Sake Dokar) ta 2021.


Ya ce majalisar kasa ta yi dokar da za ta tabbatar da cikakken cin gashin kan bangaren shari’a a matakin tarayya, yana mai kira ga majalisun dokokin jihohi da su zartar da irin wannan dokar.


Kungiyar Ma’aikatan Shari’a (JUSUN) ta bar kotuna a duk fadin kasar nan a kulle tun ranar 6 ga Afrilun 2021, don nuna rashin amincewa da rashin aiwatar da ikon cin gashin kai ga bangaren shari’a a matsayin bangare na uku na gwamnati.


Bamidele ya ce, “Abin dariya ne cewa a wannan lokacin, har yanzu muna kokawa da bukatar ba da ‘yanci ga bangaren shari’a na gwamnati a matakin jihohi da na kananan hukumomi.


“Majalisar kasa na yin dokoki wadanda za su tabbatar da cikakken ikon cin gashin kai ga bangaren shari’a a matakin tarayya.


“Majalisar kasa ba ta ba wa jihohi dokoki irin wannan karfin ba, batun yana nan makale a majalisun dokokin jihohi.


“Fannin shari’a a Babban Birnin Tarayya mai zaman kansa ne saboda mun yi abin da ya kamata mu yi. Abin da ke gaba shi ne majalisun dokokin jihohi su yi abin da ya kamata su yi.


“A ka’ida, yadda lamarin yake, mambobin kwamitin majalisar dattijai kan harkokin shari’a da ‘yancin Dan Adam sun yi kokarin ka da su kira wadanda ke zanga-zangar da su dakatar da irin wannan zanga-zangar. Ba mu son zanga-zanga amma tabbas, za mu gwammace tattaunawa da gwamnonin jihohi, majalisun dokoki da sauran masu ruwa da tsaki don yin abin da ya kamata ga biyan bukatar al’umma.


“Ba za mu iya ci gaba da yin kira ga bangaren shari’a da su ba zaman lafiya dama ba alhali mun san yanayin da suke aiki ba za su iya ba da tabbacin samar da adalci ba. Muna magana ne game da sake fasalin shari’a, muna magana ne kan bukatar sake fasalin bangaren shari’a. Wannan yana da mahimmanci ga ‘yancin bangaren shari’a a wannan kasar.”


Ya kara da cewa, “Bai kamata sauran kasashen duniya masu wayewa su bar mu a baya ba. Babu wanda zai yi hasarar komai ta hanyar bayar da ‘yanci ga bangaren shari’a a matakin jiha tun da an yi shi a matakin kasa. Gaskiyar cewa sauran ma’aikata da ma’aikatan sashen shari’a na tarayya suna shiga cikin zanga-zangar yana cikin hadin kai ne kawai ga abokan aikinsu a matakan jihohi. Lamarin kungiya ne kuma ba mu da iko a kansa.


“Muna kira ga gwamnonin jihohi da su yi abin da ya kamata saboda ‘yancin cin gashin kai na bangaren shari’a ba abin tattaunawa ba ne, abu ne da ya zama wajibi. Babu dimukiradiyyar da za ta iya rayuwa ba tare da an kafa ta bisa doka da kuma shari’a mai zaman kanta ba.” Kamar yadda ya bayyana.

Post a Comment

0 Comments