Makarantar NITT Zariya Za Ta Kera Motar Farko Mai Amfani Da Hasken Wutar Lantarki


Daga Muhammad Farouk 

Makarantar fasaha da zirga-zirga ta Nijeriya dake garin Zariya a jihar Kaduna, ta ayyana membobin 22 na kwamitin da zai fara kera motoci masu amfani da hasken wutar lantarki. 

A yayin da yake kaddamar da kwamitin a ranar Alhamis, shugaban hukumar gudanarwa na NITT, Olorogun-John Inojeharho ya ce shirin samar da motoci masu amfani da hasken wutar lantarki zai rage illolin da hayaki ke haifarwa. 

Ya ci gaba da cewa; “ayyana wannan kwamitin yana da alaka da bin umurnin ministan sufuri, Rotimi Amaechi wanda ya yi tun cikin shekarar 2019”, inji , Olorogun-John Inojeharho.

Inojeharho ya sharwaci kwamitin da ya yi aiki tukuru wajen cimma wannan manufar domin tabbatarwa da cewa aikin da aka dorawa kwamitin tabbas mai yiwuwa ne kuma za su iya. Tare da kuma daukaka darajar makarantar NITT  a taswirar duniya cewa makarantar tana daya daga cikin wadanda suka fitar da duniya daga amfani da man fetur zuwa hasken wutar lantarki a motocinsu. 

Kwamitin ana sa ran zai fito da hanyar da zai taimakawa NITT wajen samar da ababen hawa masu amfani da hasken lantarki. 

Sauran abubuwan da ake sa ran kwamitin ya gudanar sun hada da fitar da tsare-tsare da kuma samfur na ababen hawan masu amfani da hasken lantarki, da kuma fito da hanyar da za a kera su a NITT da kuma bunkasa ayyukan NITT din na samar da ababen hawan a bangaren ma’aikatar motoci ta Nijeriya. 

Har wala yau kwamitin zai fito da bayanan irin kudaden da za a kashe wajen gudanar da aikin, da kuma fito da dabarun da aikin zai dore da samun ci gaba, tare da bankado hanyoyin da za a samu gudummawa da hanyar kulla alaka da wadansu ma’aikatun bincike ko makarantu ko wata hukuma. 

Membobin kwamitin sun hada da; Bayero Salih-Farah, Babban Daraktan NITT din a matsayin shugaba, sai sauran membobin sun hada da;  Elkanah Ngbale, Daraktan lura da cibiyar fasaha ta NITT, sai Felicia Nwanosike, Daraktan makarantar zirga-zirga, sai kuma  Ibrahim Mundi, Daraktan cibiyar bayanai, labarai, laburare da kuma fasaha,  da sauran su.

Post a Comment

0 Comments