Manchester City Ta Lashe Kofin Carabao Bayan Ta Doke TottenhamManchester City ta lashe kofin Carabao, bayan doke Tottenham Hotspur da ci 1-0 mai ban haushi a wasan karshe da suka fafata a jiya Lahadi a Wembley, wanda ya samu halartar 'yan kallo dubu takwas.

Kwallon da Aymeric Laporte ya jefa mintina 8 kafin tashi daga wasan ya taimaka wa Manchester City wajen samun nasara, da kuma hana Tottenham lashe kofin bayan shekaru 13.

Wannan ne kuma karo na farko da a cikin watanni 13 aka bar 'yan kallo daga kowanne bangare suka shiga wasan da aka yi a kasar Ingila sakamakon cutar korona.

Wannan nasarar ta nuna cewar City ta lashe kofin sau 4 ke nan a jere.

Post a Comment

0 Comments