Masarautar Kauru Ta Yi Sabon Sarki


Daga Wakilinmu

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya amince da nadin Alhaji Ya’u Shehu Usman, tsohon Sarkin Fadan Kauru a matsayin sabon Sarkin Kauru.  

Sanarwar tabbatar da nadin ta fito me a sanarwar da Mr Muyiwa Adekeye, mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin kafafen watsa labarai ya fitar a ranar Asabar a Kaduna. 


Sanarwar ta ce sabon Sarkin Kauru, Alhaji Ya'u Shehu Usman ya fito ne daga gidan sarautar Wadai, inda ya gaji Marigayi Alhaji Ja’afaru Abubakar, wanda ya rasu a cikin watan Janairun 2021. 

Usman, ya kasance shugaban Hukumar 'Fiscal Responsibility Commission,' ta jihar Kaduna, an kuma haife shi a ranar 15 ga watan Mayin 1955 a garin Kauru. Ya fara aikin gwamnati ne a shekarar 1977. 

Sabon Sarkin Kauru din ya yi ritaya a aikin gwamnati a shekarar 2012 a matakin Darakta a ma'aikatar kudi ta MoFi a ofishin Babban Akawu ta jihar Kaduna. 


Sabon Sarki masani ne akan harkokin kudi, kuma tsohon shugaban karamar Hukumar Giwa ne, sannan ya rike mukamin Sakatare a karamar Hukumar Kaduna Ta Kudi, kuma babban Jami'i a karamar Hukumar Zangon Kataf. 

Tsohon memba ne a kwamitin sanya ido ta jihar Kaduna, kuma memba ne a Hukumar gudanarwa na KASUPDA. 

Post a Comment

0 Comments