Masarautar Uke Ta Bai Wa Daraktar NAPTIP Sarautar Zinariyyar Uke

 

Daga Wakilinmu

Masarautar Uke dake jihar Nasarawa a karkashin mai Martaba Sarkin Uke, Alhaji Mohammed Hassan ta yiwa Daraktar hukumar dakile safarar mutane ta kasa wato NAPTIP, Imaan Sulaiman-Ibrahim sarautar Zinariyyar Uke. 

Daraktan hulda da kafafen watsa labarai na Imaan Sulaiman-Ibrahim, Kwamared Lawal Danmusa shi ne ya tabbatar da hakan a sanarwar da ya rabawa manema labarai ciki harda MADOGARA, inda ya yi amfani da wannan damar wajen mika sakon godiyarsu ga Mai Martaba Sarkin Uke, Alhaji Mohammed Hassan, bisa zabo "shugabarmu kuma jagorarmu mai yunkurin kawo sauyi Honorabul Imaan Sulaiman-Ibrahim domin bata sarautar "Zinariyyar Uke", inji sanarwar. 

Kwamared Danmusa ya ce ba ta sarautar bai zo musu da mamaki ba duba da yadda ra sadaukar da rayuwarta wajen yiwa al'umma hidima saboda Allah. "Honorabul Imaan ta bayyana dabi'u kyawawa na al'ummar Uke wadanda mutane ne masu son junansu, girmama mutane da kuma mutunci tare da sadaukarwa wajen gudanar da ayyukan kasa da aka dora musu wanda hakan ya sanya ta zama abar alfahari ga masarautar Uke", ya tabbatar. 

Sanarwar ta ci gaba da cewa; "muna mika sakon godiya ga iyalai, 'yan'uwa da abokan arziki da kuma matasan jihar Nasarawa wadanda suka rika aiko da sakon taya murna tun bayan sanarwar yi mata nadin. Sakon ku ya sanyaya zuciyarmu kuma soyayyarku abin farin ciki ne", ya nusasshe. 

Kwamared Danmusa ya ce Hajiya Imaan na matukar godiya da soyayyar da aka nuna mata. "za ta ci gaba da godewa bisa wannan".  

Kwamared Danmusa ya ce suna da tabbacin sarautar da aka bata na Zinariyyar Uke za ta yi amfani da wannan damar wajen kawo wa al'ummar Uke ci gaba mai amfani. "Muna fatan za ku riski bukin nadin sarautar idan an sanya ranar nadin", ya tabbatar. 

"Ga uwarmu Zinariyya, muna addu'ar Allah ya taimake ki, ya ba ki kariya ta musamman da hikima a yayin da tabbatar miki da wannan sarauta", ya jaddada. 

Post a Comment

0 Comments