Daga Comr Abba Sani Pantami Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Sheikh Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, ya ce zarg...
Daga Comr Abba Sani Pantami
Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Sheikh Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, ya ce zarge-zargen cewa yana da alaka da masu tsattsauran ra'ayi karya ce kawai masu adawa da yadda yake hada layuka da katin zama dan kasa (NIN) ne ke alakanta shi da ‘yan ta’adda.
Sheikh Pantami ya fadawa jaridar Premium Times a wata hira ta musamman a ranar Juma’a, 16 ga watan Afrilu, cewa mutanen da ke adawa da yadda gwamnati ke hada lambar NIN da lambobin wayoyi sune ke yada zargin.
Ministan ya kara da cewa: “Ba na shakka game da wannan. Yana da alaƙa da lambar shaida ta 'yan ƙasa. Kun san abu daya? An fara wannan tsarin a shekarar 2011, ba ta ci nasara ba. Me ya sa? An yake ta.''
Ya yi ikirarin cewa wasu tawaga sun dauki aniyar dakatar da manufar yin rajistar shaidar zama dan kasa ga dukkan ‘yan Nijeriya da kuma wadanda ke zaune a kasar.
Ministan ya ce: "A 2015, ya fito, bai yi nasara ba. A cikin 2018 akwai lokacin da aka yi ganawa tsakanin gwamnati da kamfanonin sadarwar wayoyin hannu. Kuma a zahiri an sanar da cewa ta hanyar yarjejeniya da gwamnati, wa'adin ya kasance watan Janairun 2018. Yana nan kan yanar gizo, zan nuna maku idan kuna so. Zuwa Janairu 2018, ba a aiwatar da shi ba, saboda akwai masu adawa da shi. Akwai tawaga!"
Pantami ya bayyana cewa rajistar ta NIN ba ta ‘yan Nijeriya bane kadai. Ya ce: “Yanzu sun fara zuwa da labarin cewa mutane na zuwa daga kasashe makwabta don yin rijista".
“Abin da suka kasa fahimta shi ne cewa Lambar NIN kasa ba ta 'yan Nijeriya kadai ba ce; kowa a Nijeriya zai iya samunta."
Ministan ya bayyana cewa sharrinsu ba zai hana shi ci gaba da gudanar da aikin ba.
Ministan Sadarwa, Dakta Isa Ibrahim Ali Pantami, ya bayyana hakan ne ta bakin hadiminsa, Dr Femi Adeluyi, a ranar Alhamis a shafin Twitter.
Ministan ya ce za a cigaba da rijistan amma da sharadin sai mutum na da lambar katin zama dan kasa, NIN.
No comments