Matashiya Ta Kai Karar Marafan Mafara Bisa Zargin Jagorantar Yi Mata Auren Dole

     Alhaji Muhammad Marafan Marafa 

Daga Muhammad Farouk

Maryam Abubakar dake zaune a Mairuwa Road a garin Funtuwa ta jihar Katsina ta kai karar Hakimin Mafara dake karamar Hukumar Talata-Mafara a jihar Zamfara wurin kungiyar kare hakkin mata ta 'Women's Rights Advancement and Protection Alternative (WRAPA)', dake Abuja, a cikin takardar karar da MADOGARA ta sami kwafinta wanda Maryam ta rubutawa Babban Sakataren kungiyar ta WRAPA. 

A cikin takardar karar, Maryam ta yi zargin cewa Alhaji Muhammad Marafa na Talata Mafara, da shi da wani Bello Shehu da kuma Mande Gidan Taba sune suka shirya aurenta a boye ba tare da saninta ba. 

Takardar karar ta ci gaba da cewa; "an daura auren ne a boye da misalin karfe 11 na dare a ranar 14 ga watan Afrilun 2021 a fadar Marafan Mafara dake titin Ruwan bore Road, Opp. Town Stadium a Talata Mafara ta jihar Zamfara ba tare da amincewata ba", inji ta. 

Maryam ta ci gaba da cewa; "bayan daura auren ne labari ya riske ni cewa ni yanzu matar Alhaji Mu'awiya Dan Sakai ce". 

Takardar karar ta ci gaba da cewa; "Alhaji Mu'awiya mutum ne mai kudi a Talata Mafara, mutane sun shaide shi da auri saki a duk lokacin da ya ga dama", ta tabbatar. 

Takardar ta zargi Alhaji Mu'awiya da amfani da kudi da sanayya wajen daura aurenta da shi kamar yadda ya tsara. 

A takardar da ta aikawa WRAPA, Maryam ta labarta cewa; "Alhaji Mu'awiya ya zo wurina ya nemi zai ba ni kudi da mota, amma na ki yarda, sai ya fahimci ni marainiya ce saboda mahaifina ya rasu, shi ne yake son amfani da kudi da hanya domin ya aure ni ba tare da amincewata ba", ta tabbatar. 

Maryam Abubakar ta hakikance akan cewa daura mata aure ba tare da amincewarta ba ya sabawa 'yancinta kuma hakan ka iya jefa rayuwarta cikin hadari. 

Maryam Abubakar ta shaidawa MADOGARA cewa: ta kawo karar Marafan Mafara zuwa ga kungiyar kare hakkin mata ta WRAPA ne sakamakon kotuna ba sa aiki saboda kungiyar ma'aikatan kotu na yajin aiki. 

Post a Comment

0 Comments