Matsalar Tsaro Ba Zai Hana Inyamurai Fitar Da Shugaban Kasa A Zaben 2023 Ba -Sanata ObinnaSanata Obinna Ogba, dan majalisa mai wakiltar Ebonyi ta tsakiya daga jam'iyyar PDP, ya bayyana cewa kashe-kashen da ya auku a kwanakin nan a jihar Ebonyi da wadansu jihohin Kudu maso gabashin kasar ba zai hana su su fitar da shugaban kasa ba. 

Sanata Ogba ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a yayin da yake amsa tambayoyin 'yan jarida kan kudurin da ya gabatar a gaban Majalisar Dattawa a ranar Laraba. 

Majiyarmu ta labarto mana cewa, Sanatan ya gabatar da kudurin ne akan kashe-kashen da ya wakana a garin na Ebonyi.b

A cewar Ogba, matsalar tsaron ba zai taba zama hujjar hana su fitar da shugaban kasa ba, sabodaa cewarsa akwai matsalolin tsaro a wadansu yankunan na Nijeriya, amma hakan bai hana su ba. "Wannan ba zai zama hujjar hana Inyamurai fitar da shugaban kasa ba, ba zai yiwu ba", inji shi. 

Ya ci gaba da cewa; "ka da wani ya fake da matsalar tsaro, wannan lokacin kudu maso gabashin Nijeriya ne", ya jadadda. 

A kudurin da Ogba ya gabatar, ya nuna damuwarsa kan yadda matsalar tsaro a Nijeriya ke kara kazanta a fadin kasar. Ya kara da cewa; akwai bukatar gwamnatin Tarayya ta kawo karshen kashe-kashen da lalata dukiyoyin al'umma. 

Post a Comment

0 Comments