MATSALAR TSARO: Gwamnonin Inyamurai Sun Kafa Ta Su Rundunar Tsaron

Jaridar Dimokuradiyya ta labarto cewa; gwamnonin Inyamurai dake kudu maso gabashin kasarnan sun ayyana ƙaddamar da runduna ta musamman da za ta rika bai wa yankinsu su tsaro. Sunan rundunar tsaron da suka kafa ‘Ebube Agu’.

Bayanai sun nuna cewa; gwamnonin sun jaddada cewa har yanzu haramcin da aka sanya kan kiwo a yankin yana nan daram, inda suka umurci sabuwar hukumar tsaron ta tabbatar da an mutunta dokar da suka sanya.

Majiyarmu ta ruwaito cewa gwamnonin sun hadu ne a Owerri, babban birnin jihar Imo, inda suka tattauna da shugabannin hukumomin tsaron yankin.

Muƙaddashin babban sufeton ƴan sanda na ƙasa Usman Baba ya tura wakilansa karkashin jagorancin mataimakin Sufetan ‘yan sanda.

A ranar Litinin da ta gabata, ƴan bindiga suka farwa hedikwatar ƴansanda a Owerri, tare da kona motoci 38 da sakin fursunoni 1,844.

Post a Comment

0 Comments