Matsalar Tsaron Nijeriya Ta Dame Mu, Inji Janar Abdulsalami


Tsohon shugaban mulkin sojin Nijeriya Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ya bayyana takaicinsa kan karuwar taɓarɓarewar tsaro a kasar.

Janar Abdulsalami wanda shi ne shugaban kwamitin tabbatar da zaman lafiya na Nijeriya ya bayyana haka ne a wata hira da Editan BBC Hausa Aliyu Abdullahi Tanko.

Tsohon shugaban ƙasar ya kuma yi tsokaci akan irin ƙoƙarin da sojoji ke yi wajen tabbatar da tsaro da kuma kare hare-haren da ake kai ma jami'an tsaro a kudu maso gabashin Najeriya.

Ya fara bayani ne kan matsalar tsaron da ƙasar ke fama da ita.

Post a Comment

0 Comments