Mazauna Kauyuka A Jihar Neja Sun Sulhunta Da 'Yan Bindiga


Daga Muhammad Farouk

Wadansu kauyaku dake karamar Hukumar Shiroro ta jihar Neja da 'yan bindiga suka mamaye sun yi yarjejeniyar sulhu da 'yan bindigar domin samun zaman lafiya.

Kauyakun dai suna fuskantar hare-hare daga 'yan bindigar na tsawon watannni wanda ya kai ga mazauna kauyukan sun rasa rayukansu da dukiyoyinsu a yayin da dama ke hannun masu garkuwa da jama'a.

Shugaban kungiyar matasan Shiroro, Sani Abubakar Yusuf Kokki, ya bayyana cewa dukkanin kauyukan dake Gurmana da Manta a Shiroro din, sun yi yarjejeniyar sulhu da 'yan bindigar kamar yadda Jaridar Sahelian Times ta labarto.

Ya kara da cewa; "sun cimma yarjejeniyar biya wa 'yan bindigar wadansu kudade da sauran  bukatu da ya hada da saya musu mota kirar Honda", inji shi.

Ya ci gaba da cewa; "har wala yau, wadansu garuruwa da kauyaku dake gundumar Bassa/Kukoki sun bi sahun yin wannan yarjejeniyar akan za su biya wadansu kudade ga 'yan bindigar domin su daina kai musu hare-hare", ya tabbatar.

Jihar Neja na daya daga cikin jihohin dake fuskantar hare-haren 'yan bindiga a Arewacin Nijeriya, inda a ranar Litinin gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello ya tabbatar da cewa 'yan Boko Haram sun sanya tutocinsu a wadansu kauyukan jihar. 

Post a Comment

0 Comments