Mijin Sarauniyar Ingila Ya MutuMarigayi Yariman Birtaniya Philip ya mutu yana da shekaru 99 a duniya. 

Mijin Sarauniyar Ingila, Yarima Philip ya mutu yana da shekaru 99 a duniya kamar yadda fadar Buckingham ta sanar a yau Juma’a.

Mutuwar Yariman na Edinburg na a matsayin babban rashi ga Sarauniyar mai shekaru 94 wadda a baya ta  bayyana shi a matsayin ginshikin da ya tsaya mata a tsawon shekaru.

Ma'auratan sun kafa tarihin zama mafi dadewa suna mulkin Birtaniya. 

A ranar 16 ga watan Fabarairu aka kwantar da Marigayin a asibiti kafin ya koma gida bayan share tsawon wata guda yana jinyar ciwon zuciya.

Mutuwarsa  na zuwa ne a yayin da ya rage watanni kalilan a gudanar da bikin cikarsa  shekaru 100 da haihuwa a cikin watan Yuni mai zuwa.


Yariman ya auri Sarauniya Elizabeth a shekarar 1947, wato shekaru biyar kafin ta dare kan gadon sarautar Ingila, yayin da  ma’auratan biyu suka kafa tarihin zama masu mulki mafi dadewa kan karaga a tarihin Birtaniya.


Yarima Philip tare da matarsa Sarauniya Elizabeth cikin kuruciya AP - Kathy Willens
Ma’auratan biyu na da yara hudu da jikoki takwas da kuma tattaba-kunni 10.

Sanarwar da fadar Buckingham ta fitar ta ce, Yariman ya mutu cikin kwanciyar hankali a wannan safiyar a gidan sarautar Windsor.

Post a Comment

0 Comments