Minista Pantami Ya Ce A Ci Gaba Da Sayar Da Sabbin Layin Waya


Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, ya ba da izinin ci gaba da sayar da sabbin layukan waya da aka dakatar a Najeriya.

Pantami ya kuma sanar a ranar Alhamis, cewa za ci gaba da saurana abubuwan da a baya aka dakatar, muddin aka tantance tare da kiyaye dokokin da ma’aikatarsa da bayar na amfani da lambar NIN.

Ya za a ci gaba da yin rajistar sabbin layin ne bayan Shugaba Buhari ya amince da sabon tsarin rijistan layuka da ma’aikatar ta bullo da shi.

Ya ce tsarin ya “wajabta amfani da lambar NIN wurin yin rajistar sabon layi a ranar 14 ga Afrilu, 2021,” inji sanarwar.

Ya kara da cewa, “Sabon tsarin ya shafi sayen sabbin layin waya, bude su da kuma maye gurbinsu na kamfanoni da hukumomi da sauransu. Kuma mallakar lambar NIN sharadi ne a kowane rukuni.

Post a Comment

0 Comments