Ministan Noma Sabo Nanono Mai Shekaru 74 Ya Yi WUF Da Tsaleliyar Budurwa 'Ƴar Shekara 18


Ministan Noma da Raya Karkara, Sabo Nanono, ya auri yarinya 'yar shekaru 18 da ta bar makaranta, inda aka yi bukinsu cikin sirri kamar yadda jaridar DAILY NIGERIAN ta tabbatar.

Minista Nanono, mai shekara 74, ya auri kyakkyawar matar ne a wani takaitaccen bikin sirri da ya samu halartar wakilai uku na Ango da ke garin Jere na jihar Kaduna.

"Ministan ya sanya mutum uku ne kawai kuma ya gargade su game da bayyani game da auren ga mutane," in ji wata majiya daga dangin da ke son a sakaya sunanta.

Amaryar mai suna Rakiya, tuni ta sauka a gidan ministan a Tamandu Close da ke yankin Unguwar Nasarawa a birnin Kano.

Duk da cewa dangin ministan sun nuna adawa ga bikin, amma majiyoyi sun ce Minista Nanono ya dage kan ya auri yarinyar duk da bambancin shekaru sama da 50 da haihuwa.

“Ministan yana hauka da soyayya. Ya bayyana ba za a iya dakatar da shi ba.” In ji majiyar.

Post a Comment

0 Comments