Mutuwar Idriss Deby Za Ta Bar Gagarumin Giɓi A Yaki Da Ta'addanci, Inji Shugaba Buhari

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana Marigayi shugaban kasar Chadi Idris Deby da ‘jajirtaccen shugaba’, wanda mutuwarsa za ta bar gagarumin gibi a yakin da kasashen duniya ke yi da kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Yayin da yake bayyana kaɗuwa da kashe Idris Debby da ‘yan tawaye suka yi, Shugaba Buhari ya ce mutuwar shugaban mai shekara 68 za ta bar babban giɓi a ƙoƙarin hadin gwiwa da ake yi na murƙushe mayakan Boko Haram da kungiyar ISWAP.

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar, ta Ambato Shugaba Buhari na cewa ‘Ina cikin alhini da kaɗuwa kan mutuwar Shugaba Idris Deby a fagen daga a ƙoƙarin da yake yi na kare kasarsa.’’

Shugaban Najeriyar ya jinjina wa marigayi Idris Deby a yaƙin da yake yi da kungiyar Boko Haram, ya kuma kira shi da ‘’babban abokin Najeriya.

"Sannan ya sanya hannu a yakin da kasar ke yi da Boko Haram, wadanda suka haddasa matsalar tsaro ba a Najeriya ba har da kasashen ta makofta musamman ita kan ta kasar Chadi, da Kamaru da jamhuriyar Nijar," in ji sanarwar shugaban.

Yayin da yake yi wa al’ummar Chadi da sabon shugaban kasar ta’aziyyar babban rashin da suka yi, Shugaba Buhari ya yi kiran su hada karfi da karfe wajen murkushe masu ta da kayar baya kamar yadda rahoton BBC Hausa ya tabbatar.

Post a Comment

0 Comments