Minitan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Ali Isa Pantami ya bayyana nadamarsa kan bayanan da ya yi a baya na goyon bayan AlQa...
Minitan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Ali Isa Pantami ya bayyana nadamarsa kan bayanan da ya yi a baya na goyon bayan AlQaeda da Taliban.
Ministan dai ya fuskanci caccaka a shafukan sada zumunta bisa kalamansa da masu bayyana ra'ayi ke cewa yana goyon bayan kungiyoyin ta'addanci.
Masu ta'ammuli da shafukan sada zumunta sun nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kori Ministan idan ya ki yin murabus.
Sai dai a yayin da yake amsa tambaya a lokacin da yake gabatar da tafsiri na Ramadan na kowacce rana a Masallacin Al-Noor dake birnin Tarayya Abuja a ranar Asabar, Ministan ya ce yanzu ya fahimci wadansu abubuwan sabanin yadda ya fahimce su a jirkice a baya harma ya yi jawabi a kai. Inda ya ce dawo da zantukan na shi a yanzu har ana kamfen da su siyasa ce kawai.
"Na kwashe shekara 15, ina yawo lungu da sako na kasarnan domin fahimtar da mutane hadarin ta'addanci. Na je Katsina, Gombe, Borno da Kank harma da jihar Difa dake jihar Jamhuriyyar Nijer domin yin jawabi akan illar ta'addanci", inji shi.
Ya ci gaba da cewa; "na kalubalanci masu ra'ayin Boko Haram a wurare da dama. Na yi rubutuka da dama cikin harshen Hausa, Ingilishi da Arabiya. Na dawo da mutane da dama da suka bace zuwa hanya madaidaiciya", ya tabbatar.
Ya kara da cewa; "wadansu zantukan da na yi a shekarun baya wadanda suka haifar da cece-kuce a yanzu na yi su bisa fahimtar da na yi wa addini a wancan lokacin, kuma na sauya wadansu ra'ayin nawa da na yi a baya bisa sabbin hujjoji da suka bayyana min da kuma girma da ya zo min".
"Ina matashi lokacin da na yi wadansu jawaban; ina jami'a, wadansu bayanan nawa na yi su ne ina da kuruciya. Na fara jawabi ina da shekara 13 a duniya, Malamai da dama da daidaikun mutane ba su fahimci wadansu lamura na duniya da suka auku ba a wancan lokacin, inda suka kuma dauki matsaya, yanzu wadansu kuma sun sauya matsayarsu daga baya", ya tabbatar.
No comments