Naira Marley Ya Bayar Da Shawara Kan Yadda Za A Yi Saukan Alkur'ani Cikin Sauki A RamadanAbdulAziz Fashola wanda aka fi sani da 'Naira Marley' ya bai wa Musulmi wata muhimmiyar shawara a kafar sada zumunta ta Twitter kan yadda za a sauke Alkur'ani cikin sauki a watan Ramadana. 

Mawakin ya ce Alkur'ani na da shafuka 600, a don haka idan ka lizimci karanta shafuka 20 a kowace daya to tabbas za a kammala Alkur'ani a wata guda.

Naira Marley ya ce; shafuka 20 din ma cikin sauki za a karanta su a rana daya, musamman idan ya zama za a rika karanta shafuka hudu kacal a duk sallar farilla, to tabbas mutum zai sauke Alkur'ani cikin sauki a kwana Talatin na Azumi.

Post a Comment

0 Comments