Nijeriya Ta Fusata Da Kafa Cibiyar Twitter A Ghana

 Gwamnatin Nijeriya ta maida martani a fusace game da bude hedikwatar kafar sada zumunta ta Twitter na Afirka da ta yi a Ghana duk da cewar Nijeriyar ta zarta Ghana a yawan masu amfani da Twitter kamar yadda rahoton DW Hausa ya tabbatar.

 

Gwamnatin Nijeriya dai ta fusata da ma harzuka inda ta kai ga nuna bacin ranta a kan wannan mataki da kafar sada zumunta ta Twitter ta dauka na bude hedikwatarta a kasar Ghana maimakon Najeriyar wacce take da masu amfani da shafin har milyan 25 in aka kwatanta da mutane milyan takwas da suke amfani da Twitter a Ghana.Minsitan yada labaru da al’adun gargajiya na Nijeriyar Lai Mohammed ya dora laifi ga mutanen da ya kira marasa kishi musamman matasan da suka yi mumunanr zanga-zangar nan ta nuna bacin ransu a kan zargi na cin zarafin ‘yan sanda.

 

An dai faro zanga-zangar nuna kyama ga cin zarafin jama’a da ake zargin ‘yan sandan Nijeriyar da aikatawa ne ta kafar sada zumunta ta Twitter kafin matasan suka fito fili, su nuna ‘yar yatsa a kansu na cewa su suka jawo Nijeriya.

 

Dalilan Twitter Na Kafa Cibiyarta A Ghana A Maimakon Nijeriya


To sai dai kafar sada zumunta ta Twitter ta bayyana dalilanta na  bude hedikwatarta ta Afirka a Ghana bisa dalilai na kyautatuwar dimukurdiyya da ba da ‘yancin fadin albarkacin baki ga jama’a  musamman a kafar sada zumunta a matsayin dalilanta na bude ofishin a Ghana.Ko da yake Najeriyar ta bar masu zanga-zangar na EndSars sun yi ba tare da katsalanda ba, har sai lokacin da abin ya rikide rikici da kone-kone, amma kasar ta yi kaurin suna a game da zargi na take hakin jama’a da fadin albarkacin baki da kungiyoyin farar hula suka dade suna koken cewa hatta zanga-zanga ta lumana an sha hanasu abin da ke nuna raguwar kafa ta fadin albarkacin baki. . 


Post a Comment

0 Comments