NUC Ta Bai Wa Jami'ar MAAUN Da Jami'o'i 19 Lasisin Gudanarwa


Daga Muhammad Farouk

Hukumar lura da jami'o'in Nijeriya, NUC, ta bai wa Jami'ar Maryam Abacha American University dake Nijeriya lasisin gudanarwa a matsayin Jami'a mai zaman kanta wacce ba ta gwamnati ba. 

Jami'ar da sauran Jami'o'i 19 masu zaman kansu sun karbi lasisin gudanarwa din ne daga hannun ministan ilimi, Malam Adamu Adamu a Abuja a ranar Alhamis. 

Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, wanda ya assasa Jami'ar Maryam Abacha American University din a jihar Kano Nijeriya, shi ne ya karbi takardar shaidar lasisin gudanarwa din. 


Karbar lasisin gudanarwa din ya sanya Nijeriya yanzu na da Jami'o'i masu zaman kansu guda 99. 
 
Jami'o'in da suka karbi lasisin gudanarwa din su a yau Alhamis sun hada da; 

1. Jami'ar Mudiame dake garin Irrua a jihar Edo 
2. Jami'ar James Hope a Legas
3. Jami'ar Maryam Abacha American University of Nigeria a Kano
4. Capital City University, Kano
5. Ahman Pategi University, Pategi, a jihar Kwara
6. University of Offa, a jihar Kwara. 
7. Topfaith University, Mkpatak, a jihar Akwa Ibom. 
8  Thomas Adewumi University, Oko-Irese, a jihar Kwara. 
9. Maranathan University, Mgbidi, a jihar Imo
10. Ave Maria University, Piyanko, a jihar Nasarawa
11. Al-Istiqama University, a Sumaila a jihar Kano. 
12. Havilla University, Nde-Ikom, a jihar Cross River
13. Claretian University of Nigeria, Nekede, a jihar Imo
14. NOK University, a garin Kachia ta jihar Kaduna
15. Karl-Kumm University, Vom, a jihar Plateau 16. Mewar University, a Masaka, a jihar Nasarawa
17. Edusoko University, Bida, a jihar Niger
18. Philomath University, Kuje, a Abuja
19. Khadija University, Majia, a jihar Jigawa
20. ANAN University, a Kwall, a jihar Plateau

Post a Comment

0 Comments