Wani jigo a jam’iyya mai mulki ta APC, Cletus Obun ya ce ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami na janyo wa ja...
Wani jigo a jam’iyya mai mulki ta
APC, Cletus Obun ya ce ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali
Pantami na janyo wa jam’iyyarsu ta APC bakin jini.
Mr Obun, ya bayyana hakan ne a
hirarsa da gidan Talabijin na AIT da safiyar ranar Litinin, inda ya ce akwai
bukatar a cire Isa Pantami daga mukaminsa ko kuma ya sauka da kansa sakamakon
abin da ake zarginsa da shi na goyon bayan ta’addanci.
“Pantami ya sauka daga mukaminsa,
idan kuma ya ki sauka, a cire shi! Ka da a yarda ya ci gaba da bata sunan
gwamnatin nan”, inji shi kamar yadda MADOGARA ta labarto.
Mr Obon ya ce idan za a iya tunawa,
sauka daga mukaminta da tsohuwar ministar kudi ta yi, Kemi Adeosun ya biyo
bayan zarginta da aka yi cewa ba ta hidimtawa kasa ba (NYSC).
Kiran na Mr Obun ya biyo bayan kiran
da jam’iyyar PDP ta yi inda ta bukaci da a kori Pantami daga mukaminsa.
Shi da Isa Ali Pantami na fuskantar
wadannan kiraye-kiraye na a cire shi daga mukaminsa ne tun bayan da wadansu
kafafen watsa labarai suka wallafa wadansu bidiyoyinsa da ya yi a shekarun da
suka gabata, inda yake goyon bayan wadansu kungiyoyin ta’addanci na AlQaeda da kuma
Taliban.
Biyo bayan bayyanar bidiyon, Isa Ali
Pantami ya bayyana cewa ya yi nadamar wadannan fatawowi da ya yi sakamakon
lokacin da ya yi su yana da ‘karancin shekaru’, kuma yana da karancin fahimtar
wadansu abubuwan da suka gudana.
No comments