Rabaran Mbaka Babban Malamin Coci Ya Bukaci 'Yan Majalisa Su Tsige Buhari


Bbc Hausa ta labarto cewa; fitaccen malamin Cocin Katolikan nan da ke Nijeriya, Rabaran Fada Ejike Mbaka, ya ce ya kamata shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki idan ba haka ba a tsige shi.

Rabaran Fada Mbaka, wanda a baya a goyi bayan shugaban kasar, ya kara da cewa ya yi kiran ne saboda Shugaba Buhari ya gaza shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi Najeriya.

Malamin Cocin ya bayyana haka ne a gaban dimbin mabiyansa a Enugu da ke Kudu Maso Gabashin Najeriya.

"Idan da a kasashen da aka ci gaba ne da tuni Shugaba Buhari ya ajiye mukaminsa. Ku ambato ni a koina cewa na yi kira ga shugaba Buhari ya sauka daga mulki tun da girma da arziki.

Muna kuka ne saboda ba mu da jagora...idan ba za ka iya mulki ba, ka sauka ko a sauya ka...ko dai Buhari ya sauka da kansa ko kuma a tsige shi.."

Fada Mbaka ya kara da cewa duk da yake a baya ya goyi bayan Shugaba Buhari, ya yi hakan ne saboda a baya ya taka rawa "amma yanzu me ya sa ana kashe mutane amma babban jami'in tsarom kasa yana zaune bai ce uffan ba?"

A cewarsa 'yan bindiga suna kai hare-hare a kan kowanne bangare na kasar amma Shugaba Buhari ya gaza daukar matakin da ya dace domin shawo kan matsalar.

"Muna kira ga majalisar wakilai ta tsige shugaba Buhari. Idan kuma ta ki tsige shi ta koma fada da Fada Mbaka, to abin da ba su taba tunanin zai faru ba zai fada kan 'yan majalisar wakilai da na dattawa," in ji Malamin Cocin.


Malamin yana yin wanna kira ne a yayin da su ma masu amfani da shafukan sada zumunta a Nijeriya musamman shafin Twitter sun fusata sakamakon matakin da hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta dauka na gayyatar Dr Usman Bugaje saboda ya soki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Dr Bugaje, wanda ya yi hira da gidan talbijin na AIT a makon nan, ya caccaki gwamnatin Buhari bisa gazawarta wajen tabbatar da tsaro a kasar musamman a Arewa.

Ya yi kira ga shugaban kasar da 'yan majalisun dokokin tarayya su sauka daga mukamansu idan ba za su iya tabbatar da tsaro a kasar ba.

Post a Comment

0 Comments