Daga Wakilinmu Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya raba kayan abinci na miliyoyin naira ga mabukata domi...
Daga
Wakilinmu
Jagoran
Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya raba kayan abinci na
miliyoyin naira ga mabukata domin watan Ramadan da aka shiga kamar yadda MADOGARA
ta labarto.
Kayan
abincin ya hada da buhun suga, shinkafa da kuma masara, gero an raba su a
karkashin kulawar babban dansa, Muhammad Ibraheem Zakzaky.
Shaikh
Zakzaky wanda gwamnatin Nijeriya ke ci gaba da rike shi har na tsawon shekaru
shida tun bayan kashe mabiyansa da afka masa da sojojin Nijeriya suka a cikin
watan Disambar 2015, ya bada umurnin a raba wadannan kayayyakin abincin ne ga ‘yan
Nijeriya mabukata a cikin wannan wata na Ramadan domin saukaka musu.
Wakilinmu
ya labarto mana cewa; an raba wadannan kayayyakin abincin ne a Zariya, garin Kaduna
da kuma wadansu kananan hukumomi dake jihar ta Kaduna. Kuma wakilinmu ya
labarto mana cewa; Shehin Malamin ya kwashe fiye da shekara 20 yana irin wannan
ayyuka a duk lokacin watan Ramadan, kuma ya ci gaba da gudanar da hakan tun
bayan kama da gwamnatin Buhari ta yi. “duk da tsare shi da matarsa da gwamnati
Buhari ta yi bayan kashe dubban mabiyansa, ciki harda ‘ya’yansa uku, tare da
rauni da yake jikinsa tare da kin bin umurnin kotu da gwamnati ta yi, amma
hakan bai hana ya ci gaba da raba kayan abincin ba a duk watan Ramadan”, inji
daya daga cikin masu rabon abincin.
Har
wala yau masu rabon sun bayyana cewa Shehin Malamin ya yiwa musulmin dukkanin
duniya fatan alheri tare da murnar shiga watan Ramadan tare da yin alkawarin ci
gaba da yi musu addu’a a watan na Ramadan.
Daga
cikin wadanda suka amfana da rabon kayan abincin harda masu gudun hijira a
jihohin Zamfara da Katsina, wadanda suke baje a sansanin gudun hijira da dama a
arewacin Nijeriya.
Akalla
jihohi 13 ne suka amfana da wannan rabon, jihohin sun hada da; Sokoto, Kebbi,
Katsina, Kano, Plateau, Nasarawa da Bauchi da sauran su.
No comments