Ranar Talata Ce 1 Ga Watan Ramadan A Najeriya, Inji Sarkin Musulmi


Mai alfarma Sarki Musulmi kuma shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya ayyana ranar Talata a matsayin daya ga watan Ramadan na shekarar 1442 bayan hijira.

Hakan dai na nufin dukkan Musulmin Nijeriya za su tashi da azumi a ranar ta Talata.

Tabbacin hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Kwamitin Ganin Wata na Fadar Sarkin Musulmin ya wallafa a shafisa na Twitter.

Post a Comment

0 Comments