Rashin Adalci Da Take Hakkin Mutane Shi Ya Jefa Mu A Halin Da Muke Ciki -Arct Musa Gude


Architect Musa Saidu Gude, Jagaban garin Karshi, Nasarawa, kuma daya daga cikin jiga-jigan tafiyar da lamurra a yankin karamar Hukumar Karu dake jihar Nasarawa, ya bayyana cewar matsalar rashin adalci da ya yi ma yankin Arewa dama sauran yankuna katutu shi ne babban abin da ya jefa mu cikin yanayin da muke ciki a yanzu.

Cikin wata tattaunawa da Musa Gude ya yi da wakilinmu ya bayyana cewar matukar bamu sa hakuri da adalci, da bama kowa hakkinsa ba, kuma mu rike addu'a, to lallai ba za mu fita cikin wannan yanayin da ake ciki ba.

"Wato shi lamarin da yake yanzu ba maganar a zauna bane, lamari ne na neman a tashi tsaye, idan muka misalta da abin da ke faruwa a wasu sassan Nijeriya, mu Nasarawa lallai namu mai sauki ne sosai, ana kamanta adalci sosai, amma asalin abin da ke faruwa a kasarnan wanda a koda yaushe yake bamu ciwon kai shi ne matsalar rashin adalci, ana taka mutane da yawa, sai ka ga ga abin da mutane ke so amma sai a ce ga abin da za a kawo, kuma irin abubuwan nan zaka ga wani an zalunce shi amma sai ya yi shiru ba ruwansa, ya koma gefe yana aikata wasu abubuwa wanda jama'a ba za su sani ba."


Ya kara da cewar, "sai ka ga rikici na ta fitowa ko ina baka sani ba, sai ma a rasa meke faruwa, misalin abin da ke faruwa a yankin Zamfara da sauran garuruwa rashin adalci ya yi yawa, amma dai manyanmu, in za su yi kokari duk abin da zai faru su dinga dubawa, a dinga yin abin da talakawa ke so, kuma a yi abubuwan da zai shafi talaka, to Wallahi wani ko ka bashi bindiga ne ya yi tsiya ba zai yi ba saboda ya ga an masa abin da yake bukata", ya tabbatar. 

Post a Comment

0 Comments