Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Rashin Lafiyar Shugaba Buhari Ya 'Tsananta' -Rahoto

Daga Muhammad Farouk Jaridar Daily Trust ta labarto cewa; a ranar Lahadi ne kafafen watsa labarai suka fara tababa da tantama ka...


Daga Muhammad Farouk

Jaridar Daily Trust ta labarto cewa; a ranar Lahadi ne kafafen watsa labarai suka fara tababa da tantama kan rashin lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari. 

Shugaban kasar a ranar Alhamis dai ya dawo gida Nijeriya bayan ya je Birtaniya inda aka duba lafiyarsa. 

Mutane da dama sun nuna damuwarsu kan cewa akwai yiwuwar rashin lafiyar na shugaba Buhari ya tsananta a jiya Lahadi, wanda hakan ya sanya mutane da dama cikin firgici a tsakanin wadanda ke kusa da fadar shugaban kasa. 

An tura sakonni da dama a shafukan sada zumunta da suke lurantar da cewa jikin shugaba Buhari fa ya tsananta.

Al'umma da dama ciki harda 'yan jarida da kuma makusantan shugaban kasar, sun rika kiran waya zuwa fadar shugaban kasar a jiya, sune neman karin bayani kan lafiyar shugaban kasar. 

Sai dai da aka tuntubi Kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu kan batun, ya ki yarda ya yi magana kan rashin lafiyar shugaba Buhari. 

Majiyarmu ta Daily Trust ta labarto cewa shugaban kasar a ranar Juma'a ya halarci sallar Juma'a a Masallacin Juma'ar dake fadar Aso Rock a Abuja. 

Mafi yawan lokuta shugaban kasar ya fi zama a daki a karshen mako kamar yadda rahotanni suka tabbatar. Kuma a bana ba a yi tafsirin Ramadan da shugaban kasar ya saba halarta ba. 

A ranar 30 ga watan Maris din 2021 shugaban kasar ya tafi Landan domin duba lafiyarsa wanda ya kwashe fiye da shekara daya bai je ba. 

Shugaban kasa Buhari ya dawo Nijeriya bayan ya kwashe kwanaki 16 a Landan, inda ya shaida manema labarai bayan ya isa filin jirgin sama na sauka da tashi na Nnamdi Azikiwe dake Abuja cewa duba lafiyarsa ta shi; "ya tafi yadda ake so", inji shi. 

No comments