Rasuwar Idris Deby Rashi Ne Babba Ga Afrika -Farfesa Abubakar Gwarzo


Shugaban rukunin Jami'o'in Maryam Abacha American University (MAAUN) da 
Franco-British International University dake Kaduna, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya bayyana rasuwar shugaban kasar Chad, Idriss Deby a matsayin babban rashi ga kafatanin nahiyar Afrika. 

Farfesa Abubakar Gwarzo ya bayyana hakan ne a yayin da ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalai da 'yan'uwa na mamacin a birnin N'jamena, babban birnin kasar Chadi a ranar Litinin din 26 ga watan Afrilun 2021. 

Farfesa Gwarzo ya ce ya san mamacin Idriss Deby a matsayin jajirtacce kuma dan kishin kasa, sannan nagartaccen shugaba wanda rashinsa zai haifar da gagarumin gibi ba wa kawai ga Afrika kadai ba harma da duniya baki daya. 

A cewar Farfesa Gwarzo, Marigayin shugaban kasar Chadi za a ci gaba da tuna shi a matsayin shugaban da ya rasa ransa a fagen daga yana yakar 'yan tawayen sojoji domin kare mutuncin kasarsa. 

"A don hakan, ina mika sakon ta'aziyyata ga iyalai da 'yan'uwan Marigayin da daukacin al'ummar Chadi da Afrika da ma duniya baki daya bisa rasuwar shugaba Idriss Deby', inji shugaban Jami'ar MAAUN. 

Farfesa Abubakar Gwarzo ya yi addu'ar Allah ya jikan shugaban kuma Allah yasa aljannah Firdaus ce makoma, sannan Allah ya yiwa iyalinsa hakurin jure wannan rashin da aka yi da ba za a iya maye gurbinsa ba.  

A karshe ya yi addu'ar ci gaba da wanzuwar zaman lafiya, hadin kai da kuma ci gaba mai amfani a kasar 

Post a Comment

0 Comments