Rikicin Kabilanci: Fiye Da Mutum Dubu Daya Sun Rasa Matsugunai A Jihar Adamawa

Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa

Akalla mutum goma sha uku suka rasa ransu a karamar Hukumar Guyuk dake jihar Adamawa sakamakon rikicin kabilanci da ya barke a tsakanin kabilun dake kusa da juna a jihohin Adamawa da Gombe. 


Babban Sakataren hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Adamawa (ADSEMA), Mohammed Suleiman shi ne ya tabbatarwa da gidan Talabijin na Channels a birnin Yola dake jihar. 

A cewarsa, rikicin kabilancin ya auku ne a tsakanin kabilun kauyen Waja dake jihar Gome da kuma kauyen Lunguda dake jihar Adamawa. 

Ya tabbatar da cewa an tarwatsa kauyukan Walu, Falu da kuma Lamza, inda aka jikkata mutane da dama a sakamakon rikicin kabilancin, inda wadanda aka raunata suke karbar magani a asibitin Guyuk Cottage da sauran wuraren karbar magani a matakin farko a Guyuk din, wadanda kuma rauninsu ya girmama kuwa, suna karbar magani asibitin musamman dake Yola. 

A cewar Sakataren gudanarwa na ADSEMA fiye da mutane 1, 200 ne suka rasa matsugunansu, inda yanzu haka aka tara su a makarantar Firamare ta karamar Hukumar Guyuk dake jihar Adamawa, inda kuma ake ci gaba da yi wa wadanda suka rasa matsugunan na su sakamakon rikicin rijista a wannan sansanin na 'yan gudun hijira. 

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Adamawa, Suleiman Yahya, ya shaidawa Channels TV a Yola cewa, ba su samu rahoton adadin wadanda rikicin ya shafa ba. 

Sai dai ya ce an fara dawo da zaman lafiya da doka da oda a inda rikicin ya auku. Inda aka tura jami'an tsaro da dama a yankin. 

Rahotanni sun bayyana cewa wannan ba shi ne  karon farko da rikicin kabilancin a tsakanin wadannan kabilu ya barke ba, wanda yake kai wa ga kona gidaje da kauyuka da kashe-kashe da asarar dukiyoyi na miliyoyin naira. 


Wannan sabon rikicin ya barke ne sakamakon radadin rikicin baya da ya auku a tsakanin kabilun a shekarar da ta gabata, wanda ya yi sanadin rasa rayuka da dukiyoyi da dama. 

Post a Comment

0 Comments