SAKON BUHARI NA RAMADAN: Ku Kyautatawa Gajiyayyu

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ja hankalin al’ummar musulmi da su hada kawukansu a daidai wannan lokaci da aka shiga watan Ramadana.

Sannan ya buƙaci al’ummar Musulmin ƙasar kafataninsu da su kasance masu haƙuri da kawar da kai tare da kuma nisanta kansu da masu neman raba kan ƙasarnan ta Nijeriya.

Malam Garba Shehu, Kakakin shugaban kasar shi ne ya fitar da hakan a sanarwar taya al’ummar Musulmi murnar shiga watan Ramadana, inda ya ce shugaban na wannan kira ne a rana ta farko da soma azumin watan Ramadana.

Sanarwar ta Malam Garba Shehu, ta kuma ƙara da cewa shugaba Buhari ya roƙi ƴan ƙasar su tuna da marasa hali da mutanen da suka rasa matsugunansu wajen bada taimako da kyautatawa.

A karshe ya yi addu’ar Allah ya karbi ibadan musulmi da hada kan ƙasar da wanzuwar zaman lafiya.


Post a Comment

0 Comments