Sarkin Zazzau Bamalli Ya Bukaci A Rika Taimakawa Wadanda Ba Su Da Shi


Daga Muhammad Farouk

Sarkin Zazzau Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli ya nemi masu hali da mawadata da su rika tunawa da wadanda ba su da shi domin su taimaka musu. Sannan da su rika fitar da hakkin zakkah da kuma kyautatawa al'umma. 

Sarkin Zazzau Bamalli ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabi a taron shan ruwa na watan Ramadana da masarautar ta saba shiryawa a duk shekara, wanda ya gudana a daren jiya Alhamis. 

Wakilin Jaridar MADOGARA da ya samu halartar shan ruwan na Ramadana, ya labarto mana cewa al'umma da dama da aka gayyata wanda ya hada da Hakimai da Dagatai da masu rike da sarauta mabambanta a masarautar sun samu halartar wannan shan ruwa da Sarkin ya kira. 

Taron na shan ruwan ya kuma gudana ne a kofar Fadar Masarautar ta Zazzau. 

Tunda farko, sai da mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli ya fara da mika godiyarsa ga Allah da ya raya mu ya bada ikon shirya wannan taro. 

Sannan Mai Martaba Sarkin Zazzau din, ya mika sakon ta'aziyya bisa rashe-rashen da aka yi a masarautar cikin shekaru biyu, wanda ya ce akwai da dama da suka halarci irin taron nan na bara da bara wancan, amma a bana ba su samu damar halarta ba sakamakon Allah ya yi musu rasuwa ciki harda Marigayi Sarkin Zazzau Alhaji (Dr) Shehu Idris, inda mai Martaba Sarkin Zazzau Ahmad Nuhu Bamalli ya yi musu addu'ar samun Rahama. 

"Allah ya jikansa, Ya Rahamshe shi, ya kara masa daraja a darus salam", inji Mai Martaba. 

Mai martaban har wala yau ya mika sakon ta'aziyyarsa ga dan iyalan dan Iyan Zazzau, Alhaji Yusuf Ladan, da Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu, da kuma Abdulkadir Pate, da sauran su. 

Sarkin Zazzau har wala yau ya mika sakon godiya ga Sarkin Saminaka da ya samu halartar wannan taro duk da fama da rashin lafiyar da yake yi. 

Mai Martaba Sarkin Zazzau ya ce irin wannan taro ba yau aka fara shirya shi ba, domin ko shi ya fara halartar taron tun a shekarar 1974 tun yana yaro karami a lokacin mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Aminu. 

Dangane da gyare-gyaren da ake yi a masarautar kuwa, Sarkin Zazzau Ahmad Nuhu Bamalli ya ce wanda hakan ya batawa rai, da su yi hakuri, inda ya ce ba a yi don a batawa kowa ba, an yi hakan ne domin gyara fadar. 

Da yake tunatar da al'umma dangane da watan Ramadan kuwa, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli ya roki al'umma da su zama masu hakuri da juna, yafiya da juna wanda ya ce hakan ne zan sanya mutane su samu ci gaba. "Muna fatan mutane za su yi amfani da wannan dama wajen kyautatawa 'yan'uwa, a kulla zumunci kuma a taimaki wadanda ba su da karfi a taimaka musu", ya lurantar. 

Har wala yau mai Martaba Sarkin Zazzau, ya nemi masu aikin gwamnati da masu hali dake karkashin masarautar da su tuna da al'ummar Zariya a yayin da duk wata dama ta samu. Sannan ya nemi da a rika kula da hakkin zakkah da kuma kyauta, sannan a rika taimakon wadanda ba su da shi. 

"Wadanda suke da hanya na taimakawa mutane su samu aiki, don Allah a rika waiwayan jama'armu a gida. Ba sai an je ana gunguni ana rokon mutane ba. Idan an yi hakan za a samu nasara a cikin zaman da muke yi na tare", inji mai Martaba. 

Har wala yau da yake tofa albarkacin bakinsa dangane da matsalar tsaron Nijeriya, Mai Martaba Sarkin Zazzau Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli, ya nemi al'umma da su dage da addu'a, inda ya ce; "muna rokon jama'a a rike addu'a, saboda kowa ya san abin da yake faruwa a kasarnan, mafita a gare mu shi ne addu'a, da fatan Allah ya tsare mu ya tsare mutuncinmu." 

Mai Martaba ya ce wadanda suka taimaka taron ya yiwu cikin nasara; "Allah ya saka musu da alheri. Sauran jama'a baki daya mungode da wannan karamci da aka yi mana. Da fatan ba sai lokacin azumi kawai zamu rika haduwa gaba daya haka ba. Muna fata idan Allah ya raya mu muka samu dama lokaci bayan lokaci za a rika taruka irin wannan kawai don a gaisa da juna", inji shi. 

Inda ya nemi da taron ya zama za a rika amfani da shi don sanin halin da al'umma take ciki domin a tallafa mata. 

Post a Comment

0 Comments