Sarkin Zazzau Ya Tsige Ciroman Zazzau Mai Shekara 84

    Ciroman Zazzau, Alhaji Sa'idu Mailafiya

Labarin dake shigowa Jaridar MADOGARA na nuni da cewa; Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli ya tsige Ciroman Zazzau, Alhaji Sai'du Mailafiya daga mukaminsa bisa zarginsa da rashin da'a ga sabon Sarkin. 


Majiyarmu ta cikin Fada ta labarto mana cewa Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ya bayar da sanarwar cire Ciroman Zazzau din ne mai shekara fiye da 80 a duniya, Alhaji Saidu Mailafiya daga mukaminsa nan take.

Alhaji Sai'du Mailafiya wato Ciroman wanda aka cire, ya kasance mai shekaru 84 a duniya, inda Sabon Sarkin ya zarge shi da rashin girmama Sarkin da kuma kokarin sanyawa a yiwa sabon Sarkin bore a masarautar.

Majiyarmu ta ci gaba da cewa; fadar Sarkin sam ba zata lamunci cin dunduniya da rashin daraja ba wanda Basaraken ke nunawa Sarkin ba.

Shi dai Saidu Mailafiya Baffa ne ga sabon Sarkin Zazzau Ahmed Mailafiya.

Tuni Mai Martaba Sarkin Zazzau din, Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli Ya sabunta ma Alhaji Shehu Tijjani sarauta daga Barden Zazzau zuwa Chiroman Zazzau. 

             Sabon Ciroman Zazzau

Sai dai tuni mutane a birnin Zazzau musamman makusantan Ciroman Zazzau din da aka cire suka fara guna-guni bisa matakin Sarkin Zazzau din. 


Post a Comment

0 Comments