Shugaba Buhari Ka Yi Watsi Da Kiraye-kirayen Sauke Pantami, Cewar Gamayyar Kungiyoyin Fararen Hula

 


Gamayyar Kungiyoyi fararen hula masu kare hakki, CSOs sun yi kira da Shugaba Buhari da ya yi watsi da masu neman a sauke Dr Isa Ali Pantami , domin a cewar kungiyoyin, wasu marasa kishin kasa ne da ba su son zaman lafiya da tsaro suka dauki nauyin abin saboda a dakatar da rijistar lamabar zama dan kasa wato NIN.

Kungiyoyin sun ce Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani mutum ne mai nagarta da ke kawo sauye-sauye masu amfani a kasar.

 Gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil'adama da tabbatar da mulki na gari ta ce wasu ne suka dauki nauyin kiraye-kirayen da ake yi a kafafen sada zumunta na neman sauke ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Dr Isa Pantami da nufin kara lalata harkar tsaro a kasar.

Hadakar ta ce wadanda suka dauki nauyin abin suna ci gaba da samun riba daga kalubalen rashin tsaro da ake fama da shi a wasu sassar kasar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A jawabin da ya yi a Legas a ranar Talata 20 ga watan Afrilu, jagoran hadakar, Kwamared Declan Ihekaire, ya ce sun damu kan ganin yadda ake ci ci gaba da neman sai Pantami ya sauka.

Gamayyar ta bayyana Pantami a matsayin mutum mai nagarta da basira kuma daga cikin mutane masu muhimmanci a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Ihekaire ya ce tilas ta sa suka fito domin yin Allah wadai da bata sunan da wasu marasa kishin kasa da ke amfana da rashin tsaro ke yi wa Dr Pantami da masu adawa da batun rajistan NIN wanda zai taimakawa kasar wurin dakile laifuka da samar da tsaro.

Har wala yau, kungiyoyin sun ce sun gamsu da gaskiya irin ta Dr Isa Pantami inda ya amsa cewa a baya ya furta wasu maganganu da ake yi wa kallon goyon bayan kungiyoyin ta'addanci amma tuni girma ya zo masa kuma ya sauya tunaninsa. Don haka kungiyar ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya yi watsi da masu kiraye-kirayen ya sauke Dr Pantami kuma kada ya bari marasa kishin kasa su lalata masa gwamnati.

 

Post a Comment

0 Comments