Shugaban Majalisar Jihar Kaduna Ya Kori Hadiminsa A Kan Rahoton Batanci Ga El-Rufai

     Gwamna El-Rufai Da Rt. Hon. Zailani

Daga Bello Hamza

Ofishin Shugaban Majalisar dokokin jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Zailani ta sanar da dakatar da wani jami'in Shugaban Majalisar, Al'ameen Muhammad Sameen akan wani rahoto na batanci da ya wallafa akan Gwamna Nasiru el-Rufai na Jihar Kaduna.

Sanarwa dakatarwar yana kunshe ne a takardar manema da Ibrahim Dahiru Danfulani, Jami'i na musamman ga Shugaban Majalisar akan harkokin watsa labarai ya sanya wa hannun aka kuma raba wa manema labarai a Kaduna ranar Asabar, ya ce, dakatarwar ta fara aiki ne a nan take.

Bayani ya nuna cewa,Shugaban Ma'aikatan ofishin Shugaban Majalisar ya sanya hannun a wasikar dakatarwar, " An yanke shawarar dakatar da shi ne akan rahoton da ya wallafa a kafar safarwa ta Hausa 7 Nig, Inda ya yi wasu kalamai na batanci ga ayyukan Gwamnan jihar."

Sanarwa ta kuma yi tir da halayyar wasu kafafen watsa labarai a  Jihar Kaduna na yadda suke wallafa labarai ba tare da sun tantance ba, "Yin haka ya saba wa ka'idojin aikin jarida" inji sanarwar.

Idan za a iya tunawa kafar sadarwar Hausa 7 Nig ta wallafa rahoton inda ta ce wai Shugaban Majalisar Kaduna Hon. Yusuf Ibrahim Zailani ya ce wai tsare-tsare da manufofin Gwamna el-Rufai suna kashe al'ummar jihar Kaduna, kafar ta kuma ce wai hadimin Shugaban Majalisar, mai suna Al'ameen Muhammad Sameen ya sanar da ita.

Post a Comment

0 Comments