Sun Kashe Kusan Dubu Hamsin Wajen Karrama Dan Majalisa, Ya Ba Su Naira Dubu Sha Biyu


Wata ‘kungiyar matasa a Sakkwato sun sha mamakin da ba su taba zato ba a ranar Juma’a bayan da Honorabul Abdullahi Balarabe Salame, dan majalisar tarayya mai wakiltar Gwadbawa/Illela ya ba su gudummuwar Naira dubu goma sha biyu (N12,500) bayan sun ba shi kyautar girmamawa.

Wani daga cikin kungiyar ta matasa ya shaidawa jaridar turanci ta Daily Star cewa lalle sun kai wa Honorabul Salame ziyara kuma sun karrama shi da kyauta ta musamman, sai dai ya nuna takaicinsa na yadda dan majalisar ya bige da ba su  N12,500.

 “Ko shakka babu abin ya yi matukar ba mu mamaki wallahi domin mun kashe kudi masu yawa wajen hada kyaututtukan da mu ka ba shi. Amma kuma sai mu ka kare da Naira dubu Goma sha biyu da dari biyar”, ya lurantar.

Matashin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce ba wai sun je neman kudi ba ne a wurin dan majalisar, amma dai ba su yi tsammanin dan majalisar ya saka musu da hakan ba.

Da jaridar ta tuntubi dan majalisar, Abdullahi Salame ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce shi ya baiwa matasan dubu Goma sha biyu din su yi kudin mota, domin shi ba siyasar kudi.

“Lokacin da su ka zo na lura ba wata kungiyar kirki ba ce. Kawai sun zo neman kudi ne kuma daman can ni ba siyasar bayar da kudi na ke yi ba; na fi son na bayyanawa al’umma manufofi na idan sun aminta da ni shi ke nan”, ya nusasshe.

Post a Comment

0 Comments